Ahvaz babban birnin lardin Khuzestan ne (ma’ana Shekarestan), wanda shine birni na uku mafi girma a Iran. Khuzestan na da Birane 20 da garuruwa 47. Manufarmu ta yin wannan rubutu mai taken Karatu a Ahvaz ita ce gabatar muku da yanayin al’adu, karatu, yanayin gari, da sauransu na wannan gari mai suna Ahvaz. Wannan lardi (na Khuzestan) yana da iyaka da lardin Larstan daga arewa, lardin Isfahan daga arewa maso gabas, lardin Ilam daga arewa maso yamma, lardin Cahar Mahal daga kudu maso gabas, lardin Bakhtiyari da na Kuhgeluyeh-o-Biver Ahmad, daga kudu Khalije Fars, daga yamma kuma yana iyaka da ƙasar Iraq.
Ahvaz
Garin Ahvaz yana kudu maso yammacin ƙasar Iran ne, kuma ɗaya ne daga cikin manyan birane masu masana’antu da albarkatun man fetur. Yanayin garin kuma za a iya cewa ya kasu kashi biyu, ɓangaren duwatsu (ta arewa da gabacin garin), da kuma sararin fili (ta kudancin garin). Ahvaz na ɗaya daga cikin garuruwa masu yanayi 4 a shekara, ko wane yanayi na da irin nasa kyau.
Mutanen garin Ahvaz suna magana da yaren Farsi da kuma larabci. Bayanai sun nuna cewa, kashi 36 cikin ɗari na al’ummar wannan gari larabawa ne, kashi 16 kuma lerawan Bakhtiyar ne. Yawan mutanen garin Ahvaz mutum 3746772, iyalai 644040.
Abubuwan musamman da suka keɓanci wannan gari akwai Burya Bafi ko Hasir Bafi, Kapur Bafi, Galim Bafi, Dabino, Riɗi, Halva, Nau’o’i daban-daban na kayan tsami kamar tsamin Bandari, da sauransu.
Kamfanoni, masana’antun man fetur, da sauransu, duk akwai su a wannan gari.
Karatu a garin Ahvaz
A cikin lardin Ahvaz, akwai cibiyoyin ilimi guda 69 kuma akwai jami’a mai suna Jundishapur University of Medical Sciences, ɗaya daga cikin jami’o’i mafi inganci na wannan lardi (wannan jami’a na da matsayi na 92 a cikin jami’o’in Iran. Domin samun ƙarin bayani ku na iya ziyartar rubutunmu mai taken Karatu a Jundishapur University of Medical Sciences).
Jami’o’in Khuzestan sun keɓantu da mujalla 49 na musamman. A cibiyoyin karatu na lardin Khuzestan, an fitar da maƙalolin ilimi guda 89787, maƙalar mujalla 14114, maƙala 54073 a tarukan cikin gida, da kuma maƙala 14114 na ƙasa da ƙasa.
Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido
Garin Ahvaz na ɗaya daga cikin garuruwan nishaɗi na lardin Khuzestan masu wuraren yawon buɗe ido. A garin Ahvaz, an gina gadoji guda 9 akan kogin Karun (kogin da ya fi yawan ruwa a Iran), Hakan ta sa ake kiran Ahvaz da sunan ‘Birnin Gadoji’. Lokacin da kogin Karun ya shiga Ahvaz, garin ya kasu kashi biyu gabas da yamma. Yiwuwar jigilar kayayyaki a Karun da kuma samar da ruwan sha na birnin Ahvaz wasu dalilai ne da su ka muhimmantar da kogin Karun.
_Black Bridge
_Kerosene Bath
_Seh Ghosh University
_White Bridge
_Abdulmajid Market
_Mapar’s House
_Moin Al-Tajjar House
_Kohsaran Hill Stone Cemetery
_Preparatory School for Boys
_Kianpars Tabiat Bridge
_Karun River
_Naderi Street
_Lashkar Abad
_Ahvaz Waterfall (7th bridge)
_Tomb of Ali Ibn Mahziar
Cibiyoyin Magani
_Golestan Hospital
_Imam Khomeini Hospital
_Shahid Rajaei Hospital
_Begai Hospital
_Milad Hospital
_Mehrgan Day and Night Clinic
_Amir al-Mominin Hospital
_Fatima Al-Zahra Hospital
_Apadana Hospital
_Aria Hospital
_Salamat Hospital
_Arvand Hospital
_Abu Dhar Children’s Hospital
_Mehr Hospital
_Razi Hospital
_Ayatollah Taleghani Hospital
_Ayatollah Karmi Hospital
_Sinai Hospital
_Shafa Hospital
_Da sauransu…
Hotal Hotal
_Pars Hotel
_Oxygen Hotel
_Zagros Hotel
_Karon Hotel
_Iran Hotel
_Persia Hotel
_Naderi Hotel
_Aramesh Hotel
_Soumya Hotel
_Iranika Hotel
_Nishekar Hotel
_Hadiye Hotel
_Emarat Marmar Hotel
_Da sauransu…
Ɗakunan Karatu
_Central Library
_Sardar Shahid Ali Hashemi Public Library
_Shahid Shafi’i Library
_Shahid Beheshti Public Library
_Shahid Rajaei Library
_Shahid Chamran Central Library
_Shahid Bahnar Library
_Shahid Muftah Library
_Shahid Motahari Library
_Shahid Dastghib Library
_Da sauransu…
Cibiyoyin Kasuwanci
_Negin Shopping Center
_Royal Shopping Center
_Setila Shopping Center
_Olive Shopping Center
_Ceremonial Shopping Center
_Mahziar City Center
_Zahra Shopping Center
_Imam Reza Market
_Kianpars Tower Commercial Complex
_Karon Shopping Center
_Abdulmajid Market
_Imam Khomeini Market
_Kaveh Market
_Nakhl Plaza
_Sadaf Market
_Hirad City Center
_Marv Market
_Da sauransu…