تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Damar koyon yaren farsi ga ɗaliban waje a daidai lokacin karatunsu a Iran

Damar koyon yaren farsi ga ɗaliban waje a daidai lokacin karatunsu a Iran

Loading

A rahoton ƙungiyar kimiyya da koyarwa ta IRNA daga cibiyar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta majalisar ƙoli ta juyin al’adu, Ayatullahi Sayyed Ibrahim Raisi a wata takarda da ya aika wa ma’aikatar ilimi, hukumar lafiya, jami’ar Azad,
Jami’atul Mustafa, Bonyad Sa’adi, Sanjesh, Setade Rahbari, da sauran ƙungiyoyi masu alaƙa, ya bayyana amincewarsa da ba ma ɗaliban ƙasashen waje da suke karatu a Iran wata dama ta koyon yaren farsi a lokaci guda kuma suna ci gaba da karatunsu a ƙasar Iran. An tabbatar da wannan ƙudurin ne a wani zama mai lamba 896 na majalisar ƙoli ta juyin juya hali na al’adu da aka gudanar a ranar 24 ga watan Bahman (kalandar Iran), sannan aka sanar nan take.

Ga sanarwar kamar haka:


Ma’aikatar Ilimi, Bincike da Fasaha
Hukumar Lafiya, Jinya da Karatun Likitanci
Islamic Azad University
Al-Mustafa International University
Sa’adi Foundation
Sazman Sanjesh
Setad Rahbari

Ana sanar da amincewa da kuma izinin “bada damar koyon yaren farsi ga ɗaliban waje masu karatu a Iran a lokaci guda da karatunsu na asali da suke yi” wanda aka zartar a zama na 896 na majalisar ƙoli ta juyin juya hali na al’adu a ranar 24/11/1402 (kalandar Iran), bisa la’akari da zama na 427 da na 461 da suka gabata ranar 24/05/1402 da 17/11/1402 (bisa shawarar Setade Rahbari).

Sheɗara ta farko – Jami’o’i da manyan cibiyoyin koyarwa da na bincike masu lasisin ɗaukar ɗaliban ƙasashen waje, suna da damar sanya azuzuwa da daurori, workshop ko ayyukan bincike ga ɗalibansu waɗanda basu samu gogewar da ake buƙata a yaren farsi ba bisa la’akari da abubuwa kamar haka:

a) Dole ya zama azuzuwa ko daurorin da za a gabatar su zama na ɗaliban waje ne zalla.

b) Lazim ne ga jami’o’i da manyan cibiyoyin koyarwa ko na bincike su bi hanyoyin da suka dace wurin karɓar lasisin shirya keɓantattun azuzuwan koyar da yaren farsi ga ɗalibansu na ƙasashen waje tare da yi musu karatunsu na asali da wani yaren da ba farsi ba. Za su karɓi lasisin ne daga hukumomin da suka dace na ma’aikatar ilimi, hukumar lafiya, azad university, da sauransu.

c) Sharaɗin kammala karatu a duka matakan karatu ga duka ɗaliban ƙasashen waje shi ne karɓar amintattar takardar shaidar iya yaren farsi.

Abun lura na 1 – Ƙungiyar Bunyad Sa’adi ke da alhakin sa ido a kan aiwatar da sashen (c)

Sheɗara ta biyu – Ɗaliban PhD na buƙatar su gabatar da takardar shaidar yaren farsi kafin rubuta jarabawarsu ta ƙashe, su kuma ɗaliban fannonin likitanci kafin jarabawarsu ta daurar Basic Science.

Abun lura na 2 – Hukuncin wannan sheɗarar ya shafi iya ɗaliban da ba ƙarƙashin scholarship su ke karatu ba ne kuma za su fara karatunsu ne bayan fitar da wanann sanarwar.

Sheɗara ta uku – Duka jami’o’i da cibiyoyin koyarwa masu lasisin ɗaukar ɗaliban waje, na da wazifar hannuntawa ɗalibansu tarjamar transcript da takardun kammala karatunsu ɗauke da duka sa hannun da ake buƙata a yaren ƙasarsu tare da na farsin.

Sheɗara ta huɗu – Ƙungiyar Sanjesh (ƙungiyar tantancewa da sa ido ga tsarin koyarwa na ƙasa) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar ilimi, hukumar lafiya, jami’ar Azad, jami’ar Al-Mustafa, da Bunyad Sa’adi na da alhakin yin tsare-tsaren shirya jarabawoyin tantancewa na yaren farsi tare da miƙa su ga Setade Rahbari domin tantancewa, wata 3 bayan wannan sanarwa.

Sheɗara ta biyar – ma’aikatar ilimi da binciken fasaha, hukumar lafiya jinya da karatun likitanci, jami’ar Azad, da jami’ar Al-Mustafa, suna da wazifar gabatar da rahoton aiwatar da wannan tsarin ga Setade Rahbari a kowace shekara.

Sayyed Ibrahim Raisi
Shugaban ƙasa kuma shugaban majalisar ƙoli ta juyin al’adu

Related Posts
Leave a Reply