Kerman (da ma’anar wurin ƙoƙari da aiki tuƙuru) yana ɗaya daga cikin manyan biranen kudu maso gabashin ƙasar Iran, wanda shi ne lardi mafi girma a ƙasar. Manufarmu ta kawo muku wannan rubutun ita ce gabatar muku da bayani a kan wannan gari na Kerman, da kuma yanayin al’adu, karatu, yawon buɗe ido, da sauransu na garin.
Kerman
A aikin ƙidaye da aka gudanar na 2015, Kerman na da adadin mutane 537,718 inda aka bayyana shi a matsayin lardi mafi yawan jama’a a Iran (a halin yanzu yana da birane 23). Garin yana ɗaya daga cikin cibiyoyin ilimi da likitanci na Iran inda ake dashen gaɓoɓi. Kerman, mai tsayin mita 1756 daga saman teku (babban birni na hudu mafi tsayi a Iran), garuruwan da suke kewayensa sun ɗara shi a yanayin zafi. Garin yana cikin yankin hamada kuma yana zagaye da lardunan Khorasan, Yazd, Sistan Baluchistan, Hormozgan da Fars.
Saboda girmansa da yanayin wurin da yake, da kuma mamaye kaso 11 bisa ɗari na ƙasar Iran da ya yi, garin yana da yanayin hamada iri-iri (Shohdad da wajen birnin Bam), yanayi irin na wurare masu zafi (yankin Kohnouj da Jiroft), da kuma madaidaicin yanayi na zafi da sanyi (yankuna masu duwatsu).
kamar dai sauran garuruwan Iran, akwai sana’o’in hannu iri-iri a Kerman, waɗanda suka haɗa da; kafet ɗin saƙa, ragamar katako, saƙar arish, khos, maraq na itace, da dai sauransu. Abubuwan tsaraba na wannan birni sun haɗa da piste, Kamach Sehan, Klumpeh, Muscati Sirjan, Sohan Zarand, Falodeh da Quto.
Karatu
A garin Kerman, akwai cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 58, kuma akwai kimanin ɗalibai 110638 da malamai 4163 a waɗannan cibiyoyin. Bincike ya nuna cewa, an wallafa maƙalar ilimi guda 47291 da suka ƙunshi maƙalolin mujalla guda 9713, maƙala 39887 a tarukan ilimi na cikin gida, guda 9713 a matakin ƙasa da ƙasa, a wannan garin. Ɗaya daga cikin ingattattu kuma karɓaɓɓun cibiyoyin ilimi na wannan gari ita ce Kerman University of Medical Sciences. Za ku iya samun cikakken bayani a kan wannan cibiya a rubutunmu mai taken Karatu a Kerman University of Medical Sciences.
Abubuwan more rayuwa da wuraren yawon buɗe ido
Garin Kerman, mai tarihin dubban shekaru, yana da wasu rubutattun ayyuka kusan guda 660 da ya yi wa ƙasa (ayyuka 7 da aka yi rajista a cikin abubuwan tarihi na UNESCO), waɗanda ke bayyana kyawawan al’adu, tarihi da fasaha na Iraniyawa. A na yi wa garin Kerman kirari da ‘Jauhari na hamadar tudu ta Iran’. Abubuwa masu jan hankali na da, na halittu, al’adu, da sauransu sune:
_Prince Mahan’s Garden
_Ganj Ali Khan Bath (Museum of Anthropology)
_Bazar Kerman
_Bam Citadel
_Pardisan Ghaem Forest
_Shahdad Desert
_Zoroastrian Fire Temple (Museum of Zoroastrian Anthropology)
_Ganjali Khan Collection
_Mushtakieh Tomb (Mushtakiyeh Dome)
_Vakil Hamam
_Ganj Ali Khan School and Caravanserai
_Sardar Bazaar
_Moidi Glacier
_Herandi House (Herandi Museum Garden)
_Takht Dargah Qoli Bey
_Masjid Malik
_Masjide Jame (Mozaffari Jame Mosque)
_Gand Jebeleeh
_Girl’s Castle
_Masjid Malik
_Baghe Fathabad (Beglerbigi Garden)
_Masjide Ganj Ali Khan
_Ganj Ali Khan Mint
_Bazar Ikhtiyari
_Da sauransu…
Wani abin jan hankalin yawon bude ido na Kerman shi ne wani yanayi wanda iska da motsin rairayi ke haifar da shi kuma ba a cika samun shi a wasu yankuna ba, kuma yana daya daga cikin yanayi mafi kyau na geomorphology a Kerman.
Cibiyoyin Magani
_Afzalipur Hospital
_Hazrat Fatima (S) Hospital
_Dr. Mohammad Javad Bahnar Martyr Hospital
_Arjomand Hospital
_Al-Zahra Hospital
_Ayatollah Kashani Hospital
_Razia Firouz Hospital
_Seyyedosh Shohada Hospital
_Shafa Hospital
_Shahid Beheshti Hospital
_Imam Hossein (AS) Hospital
_Payambare Azam (pubh) Hospital
_Mehrgan Hospital
_Noorieh Hospital
_Javadal-Aime Clinic Hospital
_Samin Al-Hojaj Clinic Hospital
_Da sauransu…
Hotal Hotal
_Pars Hotel
_Gwashir Hotel
_Jahangardi Hotel
_Ikhwan Hotel
_Hazar Hotel
_Tourism Complex
_Kermania Hotel
_Assam Apartment Hotel
_Hiva Apartment Hotel
_Klias Hotel
_Nice Hotel
_Parsi Lodge
_Pooya Hotel
_Vakil Caravanserai Hotel
_Da sauransu…
Ɗakunan Karatu
_Open Public Library
_Central Library
_Imam Reza Library
_Shahid Beheshti Library
_Herandi Public Library
_Jame Mosque Public Library
_Motahari library
_Masjid al-Nabi (PBUH) Public Library
_Shahid Motahari Public Library
_Shahid Bahonar Public Library
_Marwa Library
_Seyyed Javad Shirazi Public Library
_Shahid Abbas Sultanzadeh library
_Yazdani Fard Public Library
_Da sauransu…
Cibiyoyin Kasuwanci
_Saleh Al Mahdi Commercial Complex
_Star Bazaar
_Shafa Commercial Complex
_Ganj Ali Khan Market
_Phaeton shopping Center
_Atlas Shopping Center
_Emerald Plaza
_Da sauransu…