Idan kuna son yin karatu a Iran amma kuma kuna shakka saboda tsadar kuɗin makaranta, zaku iya yin nazari a kan karatu a wannan jami’a ta Babol Noshirvani University. Babol Noshirvani University jami’ar fasaha ce a Iran kuma ɗaya ce daga cikin jami’o’in Iran mafi muhimmanci, kuma tana da muƙamin jami’a ta ɗaya a jami’o’in fasaha na Iran. Jami’ar tana cikin jami’o’in da ke mutunta ƙa’idojin ilimi. Za mu kawo muku ƙarin bayani a kan wannan jami’a a cigaban wannan rubutu.
Gabatarwa a kan Jami’ar Babol Noshirvani
Babol Noshirvani University of Technology jami’ar gwamnati ce a garin Babol, lardin Mazandaran wadda aka assasa a shekarar 1971. A halin yanzu akwai ɗalibai 5800 da malamai 200 a wannan jami’a. Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu, wannan jami’a ta wallafa maƙalar ilimi guda 6180 a taruka da wallafe-wallafe na cikin gida. Jami’ar fasaha ta Babol Noshirvani ta wallafa mujalla 2 na musamman kuma an gudanar da taruka 9 a cikin wannan jami’a. Baya ga haka, jami’ar ta wallafa karɓaɓɓun maƙaloli guda 4787 a matakin ƙasa da ƙasa.
Jami’ar na da kwasa-kwasan karatu 70 a matakai uku; digiri, mastas, da PhD wanda ɗalibai 6500 suke karantawa yanzu haka.
Martabar Jami’ar Babol Noshirvani
Cibiyar Times a tsarin ranking da ta fitar na shekarar 2021, ta yi nazari a kan jami’o’i, cibiyoyin koyarwa da na bincike guda 1500 na duniya, a shekarar 2022 kuma guda 1662. A wannan tsarin na martaba jami’o’i (ranking) ta yi la’akari da abubuwa 4 ne; karatu, bincike, yaɗa ilimi, da kuma kimar jami’a a idon duniya.
Bisa dogaro da tsarin ranking ɗin jami’o’in duniya na TIMES (The World University Ranking 2022), Jami’ar Babol Noshirvani ta samu matsayi na farko a cikin jami’o’in Iran, da matsayi na 401-500 a cikin duka jami’o’in duniya. Yana da kyau ku san cewa jami’o’i 58 ne kawai suka samu shiga wannan ranking ɗin daga ƙasar Iran.
Har ila yau, jami’ar ta samu matsayi na 901-1000 a tsarin ranking na Shanghai.
Makarantu da kwasa-kwasan jami’ar Babol Noshirvani
Jami’ar Babol Noshirvani na da makarantu (kwaleji) guda biyar. Makarantar Mechanical Engineering wadda ta ƙunshi kwasa-kwasai kamar Mechanical Engineering, Materials Engineering (Metallurgy), da Industrial Engineering. Makarantar Electrical and Computer Engineering mai kwasa-kwasan Electrical da Computer Engineering, Makarantar Chemical Engineering, Makarantar Civil Engineering mai kwasa-kwasan Civil Engineering, da Mapping Engineering, Sai kuma Makarantar Basic Sciences wadda ita kuma ta ƙunshi kwas ɗi Mathematics, Physics da Chemistry. Da yawan kwasa-kwasan jami’ar ana yin su ne a matakan digiri da mastas kawai, sai ‘yan kaɗan da suke da har PhD.
Faculty of Mechanical Engineering
A wannan kwalejin ana yin kwas ɗin Mechanical Engineering har zuwa matakin PhD, shi kuma kwas ɗin Materials Engineering da Industrial Engineering ana yin su zuwa matakin Masters. Daga cikin membobin tsangayar ilimi na wannan jami’a akwai memba 38 na dindindin (professor 6, associate professor 8, mataimakin professor 22, da masu horarwa 2).
Heat and Fluid Department (professor 4, mataimakin professor 1, da malamai 4).
Department ɗin Solid Design and Shipbuilding Engineering (associate professor 3, mataimakin professor 7).
Department ɗin Manufacturing and Production Training (professor 2, associate professor 1, mataimakin professor 4, da malamai 2).
Department ɗin Materials Engineering and Metallurgy (associate professor 3, da assistant professor 4)
Department ɗin Industrial Engineering (mataimakin professor 6, ɗalibin PhD 1)
Fuskoki masu muhimmanci a makarantar Mechanical Engineering
Muhandis Muhammad Majdara, wakilin majalisar ƙoli ta jamhuriyar musulunci
Prof. Dawood Domiri Ganji, fuska mai muhimmanci a lardin Mazandaran, fitaccen masanin kimiyya na duniya kuma shigaban gidauniyar Elite ta lardin Mazandaran
Prof. Mufid Gorji Bandapi, muhimmiyar fuskar lardin Mazandaran a shekarar 2013
Abubuwan Alfahari
Daga cikin nasarorin Babol Noshirvani University akwai:
- Samun laƙabin ‘babban mai bincike na ƙungiyar tsarin gine-ginen ta ƙasar’ da Farfesa Ali Akbar Ranjbar ya yi a 2013
- Samun lambar yabo mai daraja ta uku a bincike na ƙasa wanda Shugaban ƙasar na lokacin Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya gabatar ga Farfesa Davoud Doumiri Ganjid a shekarar 2013.
- Ƙera robot mai suna IR141 da ƙungiyar ɗalibai na kwalejin Mechanical Engineering suka yi a ƙarƙashin jagorancin Dr. Morteza Dredel da Dr. Rozbeh Sheft
- Lashe kambun farko a zagaye na biyu na gasar tseren jiragen ruwa masu tunani a ƙarƙashin jagorancin Dr. Rouzbeh Shafqat da Dr. Morteza Dredel
- Lashe kambun farko na gasar mota ta Sokhtiba wanda Farfesa Mohsen Shakeri da Dr. Korosh Sediqi suka yi
- Samun laƙabin ‘Muhimmiyar fuskar lardin Mazandaran’ wanda Farfesa Mofid Gorji ya yi a 2010
- Ƙera jirgin sama mara matuƙi a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mofid Gurji da Dr. Ali Moazzami Gudarzi
- Samun laƙabin muhimmiyar fuskar lardin Mazandaran wanda Farfesa Dawood Doumiri Ganjid ya yi a 2008
- Ƙera software na gwajin polymer da methanol a ƙarƙashin kulawar Farfesa Ali Akbar Ranjbar
- Samun lambar yabo a kan maƙala mafi kyau ta shekarar 2008 ta daga ƙungiyar England Institute of Mechanical Engineers, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mohammad Bakshi
- Lashe lambar yabo ta zinare da kyautar sashe na musamman a gasar ƙirkire-ƙirkire ta duniya a shekarar 2008 a ƙasar Poland, wanda ɗalibin jami’ar yayi tare da jagorancin Dr. Seyed Mahmoud Rabiei
Faculty of Chemical Engineering
A wannan kwalejin, akwai kwasa-kwasan Chemical Engineering da Biotechnology a duka matakan karatu, kwasa-kwasan ‘Design of Oil and Gas Industry Processes’ da ‘Food Industry’ kuma iya matakin mastas suka tsaya. Wannan kwalejin na da ma’aikatan sashen koyarwa kamar haka; mutum 19 ma’aikatan dindindin (professor 3, associate professor 4, assistant professor 10, da mai horarwa 1).
Fuskoki masu muhimmanci na wannan kwalejin
Prof. Mohsen Jahanshahi, mamallakin lambar girma ta ƙasa mai daraja ta uku.
Prof. Qasim Najafpour, mawallafin fitaccen littafin shekarar 2008 a fannin Engineering da Applied Sciences
Abubuwan Alfahari
Daga cikin nasarorin Babol Noshirvani University akwai:
- Bayar da lambar yabo mai daraja ta uku na bincike na ƙasa wanda shugaban ƙasar na lokacin, Dakta Mahmoud Ahmadinejad, ya ba Farfesa Mohsen Jahanshahi a shekarar 2013.
- Lashe matsayi na farko da na uku a gasar badminton ta jami’a, ta ɗaliban Kwalejin Chemical Engineering a 2009
- Samun matsayi na biyu a gasar ƙwallon ƙafa ta jami’a, ta ɗaliban Kwalejin Chemical Engineering a shekarar 2009
- Dr. Morteza Hosseini ya lashe matsayi na farko a gasar table tennis ta malamai da ma’aikata na yankin a shekarar 2009.
- Samun matsayi na biyu a gasar kokawa ta yanki ta ɗaliban kwalejin Chemical Engineering a 2008
- Samun matsayi na biyu a gasar Badminton na yanki na 8 na ƙasar da ɗaliban tsangayar kimiyyar ƙere-ƙere a shekarar 2008 suka yi
- Samun matsayi na huɗu a fuskoki masu tasiri na lardin Mazandaran, wanda Farfesa Mohsen Jahanshahi ya yi a 2008
- Samun matsayi na biyu da ƙungiyar binciken Nano Biotechnology ta yi, a tsakanin cibiyoyin kimiyya da bincike 200 na duniya a shekarar 2008
- Lashe matsayi na farko a zaɓen tsari mafi kyau a fagen wadata na lardi, wanda Farfesa Mohsen Jahanshahi ya yi a 2007
- Samun matsayi na farko da Cibiyar Nazarin Kimiyyar Halittu ta Nano Biotechnology ta yi tsakanin cibiyoyin jami’a, cibiyoyin bincike da cibiyoyin gwaje-gwaje a faɗin kasar a 2007
- Tawagar jami’ar a ƙarƙashin jagorancin Dr. Majid Taghizadeh ta lashe gasar motocin sinadarai a ƙasar China a shekarar 2007.
- Samun matsayi na uku a ayyukan raya ƙasa a bikin Khorez wanda ɗalibin Chemical Engineering Fouad Mehri ya yi, ƙarƙashin jagorancin Dr. Majid Taghizadeh a 2007
- Zaɓar fitaccen littafin fasaha na ƙasar mai suna ‘Biochemical Eng. and Biotechnology’ wanda farfesa Qasim Najafpour ya rubuta a shekarar 2007
- Lashe matsayi na ɗaya a gasar motar sinadarai ta ɗaliban ƙasar wanda tawagar kimiyya ta jami’ar ta yi ƙarkashin jagorancin Dr. Majid Taghizadeh a shekarar 2006.
Kwalejin Electrical and Computer Engineering
A wannan kwalejin akwai kwas ɗin Electrical Engineering (electronics, power, control and communication) da Biomedical Engineering zuwa matakin PhD, da kuma kwas ɗin Computer Engineering zuwa matakin Masters. Ma’aikatan sashen koyarwa na wannan kwalejin sun haɗa da; membobi 40 na dindindin (professor 2, mataimakin professor 2, associate professor 28, ɗalibin PhD 1, masu horarwa 3).
Abubuwan Alfahari
Daga cikin abubuwan alfahari na wannan kwalejin akwai:
Samun matsayi na farko a jarrabawar shiga jami’a ta ƙasa a fannin Electrical Engineering (electronics, telecommunications, medical and control engineering) da ɗalibin jami’ar ya yi a shekarar 2009 .
Samun matsayi na farko a jarrabawar shiga jami’a a matakin masters ta ƙasa a fannin Computer Engineering (artificial Intelligence) da ɗalibin jami’ar ya yi a 2013.
Kwalejin Basic Sciences
A wannan kwalejin ana gabatar da kwasa-kwasan Mathematics, Physics, da Chemistry har zuwa matakin Masters. Tsangayar ilimi ta wannan kwalejin ta ƙunshi membobi 23 na dindindin.
Sashen koyarwa na Mathematics (mataimakin professor 2 da associate professor 9)
Sashen koyarwa na Physics (mataimakin professor 1, associate prof. 7)
Sashen koyarwa na Chemistry (mataimakin prof. 4, masu horarwa 2)
Nasarorin Babol Noshirvani University of Technology
Daga cikin nasarorin wannan kwalejin akwai:
Samun matsayi na huɗu a gasar ƙananan ayyuka na ƙasar karo na 8 tare da tikitin shiga gasar duniya ta ƙungiyar Simorgh ƙarkashin kulawar Dr. Reza Khanbabaei. Shekarar 2013
Samun matsayi na 6 a gasar ‘Kami Karan’ ta ƙasa karo na 8 tare da samun tikitin shiga gasar duniya da ƙungiyar Oksin, ƙarƙashin kulawar Dr. Mohammad Asdalahi Babli. Shekarar 2013
Cibiyar binciken fasaha ta Nanotechnology
An buɗe ɗakin gwaje-gwaje (laboratory) na bincike a kan Nanobiotechnology a Jami’ar Fasaha ta Babol (Noshirvani), a shekarar 2005. Ta hanyar gabatar da ayyukan kimiyya da bincike, aka mayarda wannan rukunin binciken Sashen Binciken Fasahar Nanobiotechnology a 02/03/2009. Bayan ci gaba da ayyukan kimiyya, nazari da bincike a wannan sashen, sashen ya ƙara haɓaka a shekara 2009 inda ya koma cibiyar binciken nanotechnology.
A cikin wannan cibiyar bincike, akwai sashen nano-biotechnology, nano-membrane da nano-computing waɗanda suka ƙunshi ɗakunan gwaje-gwaje daban-daban a fannin. Daga cikin manufofi da fannonin bincike na wannan cibiyar, akwai gano amfanin abubuwa masu tsarin nanostructure, kayan aikin nanotools da tsarurrukan nanosystems a masana’antu daban-daban na ƙasar kamar na likitanci, magani, tsaro, muhalli da sauransu. A wannan cibiyar akwai membobi 40 na dindindin (professor 6, mataimakin professor 7, associate professor 8 da ɗaliban postgraduate 20).
Kuɗin Makarantar Babol Noshirvani University of Technology
Abubuwan more rayuwa na Babol Noshirvani University of Technology
Wuraren Kwana:
- Wurin kwana na Aminiyan (na ɗalibai maza): yana nan a gefen jami’ar. Yana da sassa (block) 3 kuma yana da yalwataccen fili kore a ciki, tare da kayan wasanni da wurin gina jiki, zauren table tennis, filin ƙwallon ƙafa da volleyball, ɗakin wanki ɗauke da injin wanki, da wurin cin abinci. A kowane ɗaki akwai wifi, firiji, fanka, na’urar ɗumama wuri, kafet, katifa, teburi da aƙalla kujera biyu.
- Block 1: Na ɗaliban digiri da suke shekarar farko, hawa uku ne, rukunin wurin wanka na gama-gari, masallaci, kitchen guda 2, ban ɗakai 6 suma na gama-gari a kowane hawa, kowane ɗaki ya na ɗaukar mutum 4 ne kawai.
- Block 2: Na sauran ɗaliban digiri, yana da ɗakunan mutum 2 da na mutum 6, hawa uku ne, yana da masallaci, rukunin wurin wanka na gama-gari, ɗakin karatu, ɗakin kwamfuta, kowane hawa yana da kitchen biyu da ban ɗakai na kowa da kowa, mafi yawan ɗakunan hawa na biyu da na uku suna da baranda.
- Block 3: Ɗaliban da suka kammala digiri, yana da ɗakin karatu, masallaci, duka ɗakunan na mutum 4 ne kowane ɗaki yana da na’urar sanyaya wuri (ac), hawa huɗu ne kowane hawa yana da kitchen biyu da wurin wanka da ban ɗakai na gama-gari, kowane ɗaki yana da baranda.
- Wurin kwana na Raihane (na ɗalibai mata): Shima yana kusa da jami’ar kuma block ɗaya gareshi.
- Wurin kwana na Kowsar: Yana da tazara daga jami’a.
Internet :
Internet kyauta ne ga dukkan ɗaliban wannan jami’a wanda za su iya amfani da shi a harabar jami’ar da kuma hostel ɗinsu. Yawa da saurin internet ɗin ya danganci matakin karatun ɗalibi.
Abinci:
Akwai kantin abinci biyu a cikin harabar jami’ar (na mata da na maza), sannan a kowane hostel (Aminiyan, Raihane, da Kowsar) ma akwai kantin abinci. Sabis ɗin abinci (self) na jami’ar bayan ranakun juma’a, a kowace rana yana aiki, wato a kowace rana ɗalibai za su iya yin rizab ɗin abinci, sannan a kowane lokacin abinci (na rana ko na dare) akwai abinci kala biyu saboda kowane ɗalibi ya zaɓi wanda ransa yake so. A kwanakin watan Ramadan kuma ana bada abincin sahur da na buɗa baki. Haka kuma ana ƙara yawa da ingancin abinci a waɗannan kwanaki masu albarka.
Kiwon lafiya
A cibiyar kiwon lafiya da jinya ta jami’ar, akwai babban ofishin likitoci da ofishin likitan haƙora, haka nan kuma akwai ƙwararrun masana ilimin halayyar dan adam da dama da suke yi wa ɗalibai hidima.
Adireshin Babol Noshirvani University of Technology
Adireshi: Mazandaran – Babol – Titin Shariati – Babol Noshirvani University of Technology
Tambayoyin da aka yi game da Babol Noshirvani University
- Yaya ake biyan kuɗin makaranta a wannan jami’a ta Babol Noshirvani?
Ana biyan kuɗin makaranta a dala kuma a farashin kasuwa. - Shin wannan jami’a tana karɓar ɗaliban ƙasar waje a duka matakan karatu?
A a, jami’ar Babol Noshirvani tana karɓar baƙin ɗalibai ne a matakin masters da PhD kawai.
[neshan-map id=”33″]