Shahid Bahonar University of Kerman (Jami’ar Shahid Bahonar ta Kerman) ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati na ƙasar Iran. Jami’ar na kudu maso gabas ta garin Kerman, a wani wuri mai girman murabba’in mita 5,000. Tana daga cikin manya-manyan jami’o’i kuma jigogi a Iran, hakazalika ɗaya ce daga cikin fitattun jami’o’i a duniya. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan jami’ar ta Shahid Bahonar.
Gabatarwa
Jami’ar Shahid Bahonar jami’a ce ta gwamati a garin Kerman, a lardin Kerman wadda aka assasa a shekarar 1972. A halin yanzu akwai ɗalibai 19000 da malamai 1160 a jami’ar. Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi guda 20938, da guda 7835 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Shahid Bahonar ta mallaki lambar yabo kuma ta wallafa mujallu 19. Zuwa yanzu an gudanar da taruka 57 a cikin wannan jami’a. A shekarar 2023, mafi yawan maƙalolin da aka wallafa a wannan jami’a sun ƙunshi kalmomin “students” da “PCR” a matsayin muhimman kalmomi.
Jami’ar Shahid Bahonar na da haraba guda biyu manya a cikin garin Kerman, da kuma wasu ƙananun harabobi warwatse a cikin lardin Kerman kuma ana yin sama da kwasa-kwasai 100 mabambanta a jami’ar, a duka matakan karatu tun daga digiri har zuwa PhD. Ana kan ƙoƙarin mayar da ƙananun harabobin wannan jami’ar zuwa jami’o’i masu zaman kansu.
Martabar Jami’a
Jami’ar Shahid Bahonar ta samu shiga jerin fitattun jami’o’i 10 da majalisiar ƙoli ta sauyin al’adu ta lissafa a shekarar 2021. (wannan karon an yi ranking ɗin jami’o’in fasaha daban)
Tsarin ranking na TIMES ya bayyana jami’ar Shahid Bahonar ta Kerman a jerin zakarun jami’o’i 29 na ƙasar Iran a ranking ɗinsa na shekarar 2019, sannan ya sanya jami’ar a cikin jami’o’i 1258 mafi kyau na duniya.
A shekarar 2020 kuma, jami’ar Shahid Bahonar ta samu shiga sahun fitattun jami’o’i 40 na ƙasar Iran, inda ta shiga sahun 1396 na duniya.
Tsarin ranking na Leiden kuma ya bayyana jami’ar a cikin fitattun jami’o’i 23 na ƙasar Iran, da jami’o’i 938 na duniya a shekarar 2018.
Har ila yau, tsarin na Leiden ya sanya jami’ar Shahid Bahonar a sahun fitattun jami’o’i 26 na Iran, da fitattu 963 na duniya a shekarar 2019.
Kuɗin makarantar Jami’ar Shahid Bahonar ta Kerman
Grade | educational group | Farsi speakers | Non-Persian speakers |
---|---|---|---|
Bacholar | Humanities | Rial80,000,000 | €360 |
Bacholar | Other | Rial100,000,000 | €400 |
Masters | Humanities | Rial140,000,000 | €700 |
Masters | Other | Rial170,000,000 | €750 |
PhD | veterinary medicine | Rial200,000,000 | €750 |
PhD | Humanities | Rial280,000,000 | €970 |
PhD | Other | Rial340,000,000 | €1,150 |
Makarantu
- Faculty of Technical Engineering
- Faculty of Literature and Humanities
- Faculty of Agriculture
- Faculty of Mathematics and Computer
- School of Basic Sciences
- Faculty of Law and Theology
- School of Veterinary Medicine
- School of Management and Economics
- Faculty of Physics
- School of Physical Education and Sports Sciences
- Saba Faculty of Art and Architecture
Wuraren bincike
- Plant Production Technology Research Institute
- Energy and Environment Research Institute
- Research Institute of Islamic and Iranian Culture
- Mineral Industries Research Institute
- Earthquake Research Center
- Mahani Math Research Center
- Computer Engineering
- Mechanical Engineering
- Chemical Engineering
- Civil Engineering
- Mining Engineering
- Industrial Engineering
- Materials Engineering and Metallurgy
- Oil and Gas Engineering
- Persian Language and Literature
- Information Science and Epistemology
- Social Sciences
- Educational Science
- Geography
- History
- Psychology
- Foreign Languages
- Biosystem Mechanical Engineering
- Soil Science Engineering
- Production Engineering and Plant Genetics
- Plant Medicine Engineering
- Horticultural Science Engineering
- Biotechnology Engineering
- Agricultural Economics Engineering
- Animal Science Engineering
- Food Industry Engineering
- Applied Mathematics
- Pure Mathematics
- Teaching Mathematics, Computer Science, Statistics da sauransu…
Yawan kwasa-kwasan da ake yi a kowane department:
- – Human Sciences: kwas da fanni 67
- – Basic Sciences: kwas da fanni 86
- – Engineering & Technical: kwas da fanni 62
- – Agricultural Sciences: kwas da fanni 45
- – Veterinary Medicine: kwas da fanni 10
- – Art: kwas da fanni 9
- – University Campus: kwas da fanni 34
Cibiyoyi da wuraren bincike
- Plant Production Technology Research Institute
Duba da cewa lardin Kerman yana taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa tsirrai da itatuwa, kuma shi ne na ɗaya a wurin safarar kayan amfani idan aka ɗebe man fetur, musamman wurin noman dabino, pistachio, wallnut, lemu, kayanmiya, jaliz, kayan sakai, tsirran magani da na masana’antu, aka buɗe cibiyar bincike a kan dabino a wannan jami’a ta Shahid Bahonar a shekarar 1990. Bayan nan, a shekarar 1994 an samar da cibiyar bincike ta Horticulture ɗauke da department uku na Medicinal Plants, Dates, da Citrus bisa amincewar ƙungiyar bunƙasa karatun gaba da sakandare kafin a karɓi zaunannen lasisi wa cibiyar duk a cikin shekarar ta 1994.
- Mineral Industries Research Institute
Cibiyar na gudanar da ayyukanta a department uku, tare da ma’aikatan tsangayar ilimi sama da 40. Sharhin ayyukan kimiyya da bincike na cibiyar: 1. Wallafa mujallar ‘Separation Science and Engineering’ tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Chemical Engineering tun daga shekarar 2009, da samun martabar binciken kimiyya daga ma’aikatar ilimi. 2. Aiwatar da babban tsarin bincike na ƙasa wanda aka kashe wa kuɗi kimanin riyal biliyan 10, da kuma ƙulla kwangila da yarjejeniyar fahimtar juna don aiwatar da sababbin ayyukan masana’antu, mai bajet ɗin kuɗi kimanin riyal biliyan 20. 3. Wallafa sama da maƙala 200 da sunan ISI a tsawon shekaru 3 da suka gabata, da wallafa littafai 7, da gabatar da sama da maƙala 300 a tarukan kimiyya.
- Research Institute of Islamic and Iranian Culture
A shekarar 2000, bayan shawarar Engr. Shahrokh Wafadari da Dr. Muhammad Ali Mirzaei akan ƙarfafa karatun bincike na kimiyya da na jami’a musamman a ɓangaren al’adu da tsofaffin yarukan Iran, aka fara shirin samar da wannan cibiya a cikin jami’ar Shahid Bahonar ta Kerman. Cibiyar bincike akan al’adu da tsoffin yarukan Iran ta fara aiki a cikin Faculty of Literature ta jami’ar Shahid Bahonar a ranar 14/02/2001 kafin a kammala aikin ginin ta mai girman murabba’in mita 200 a Pardize Afzalipoor da ke cikin jami’ar a shekarar 2008.
- Mahani Math Research Center
An assasa ta a shekarar 1990 aka kuma canja mata suna zuwa sunan Abu Abdullah Muhammad Isah Mahani, wani masanin mathematics da aka yi a ƙarni na tara a garin Kerman. Cibiyar na gudanar da ayyukan bincike da tarukan bita a fannonin Statistics, Maths, Computer Science, tare da laccocin sati-sati, tarukan ƙarawa juna sani tsakanin ƙwararrun masana na ciki da na wajen Iran.
- Earthquake Research Center
An assasa wannan cibiyar a shekarar 1997 a cikin jami’ar Shahid Bahonar. An karɓa mata lasisi a shekarar 2011. Cibiyar na da department biyu: Geodynamics da Electromagnetic prediction of earthquakes. A halin yanzu wannan ciniyar tana da na’urar Seismometer guda biyu, da sansanin seismography guda ɗaya (a jejin gha’em na garin Kerman).
- Women and Family Research Group
- Microbiology Research Group
- Energy and Environment Research Institute
- Cibiyar bincike ta Kashigar Geomechanics Research Center wadda ita ce laboratory na rock mechanics mafi yawan kayan aiki ingantattu (irinsu; automatic direct cutting machine, automatic uniaxial and triaxial loading machine, comprehensive loading machine for bending…) a kudancin ƙasar Iran, kuma laboratory ɗin zai iya amfanar duka ma’adanan ƙasar wurin ƙayyade ma’aunan duwatsun ma’adanai.
Abubuwan More Rayuwa
- Multipurpose Hall guda biyu
- Zauren taro
- Filin wasan ƙwallon ƙafa na haki
- Filin gudu
- Filin yashi na wasan volleyball
- Filin wasan tennis
- Sansanin kiwon lafiya na hostel
- Rukunin filayen wasan volleyball,Handball, da Basketball.
Wuraren kwanan jami’ar
Wuraren kwanan wannan jami’a suna cikin harabar jami’ar ne ta ɓangaren kudu maso yamma, dukda cewa akwai ɗan nisa tsakaninsu zuwa cikin asalin jami’a, amma suna kusa da wani sashe na jami’ar. Su kuma ɗaliban likitanci hostel ɗinsu na ta ɓangaren junction ɗin Chubar. Sauran kwasa-kwasai kuma, hostel ɗin ɗalibai mata yana gaba da hostel ɗin maza da hostel ɗin ɗalibai masu iyali, kuma yana da gini 6 masu hawa 3 wanda biyu daga cikinsu sun keɓanci ɗaliban masters da PhD ne kawai. Kowane hawa yana da kusan ɗakuna 15 kuma an tsara gine-ginen ta yadda daga hawa na uku na kowane gini za a iya shiga gini na gaba.
Yanayin Wuri
Jami’ar Shahid Bahonar na nan a kudu maso gabacin garin Kerman, a kusa da babbar hanyar Bagh Gharar, nesa da tsakiyar gari. Hanyar Haft Bagh ita ce ta sada garin Kerman zuwa garin Mahan wanda ke cike da abubuwan buɗe ido.
Adireshi: Kerman, Babbar Hanyar Imam Khomeini, Meidane Pajohesh
Shafin jami’a:https://uk.ac.ir