Jami’ar Khalije Fars Jami’ar Khalije Fars jami’ar gwamnati ce kuma cibiyar koyarwa mafi girma a lardin Bushehr wadda ke cikin garin Bushehr, kuma wadda aka kafa bayan ziyarar da jagoran juyin juya hali na ƙasar Iran wato Sayyid Ali Khamena’ei ya kai a lardin na Bushehr a shekarar 1991. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai dangane da yanayin karatu a wannan jami’a ta Khalije Fars.
Gabatarwa
Wannan jami’a ta fara aiki ne a watan May na shekarar 1992 tare da karɓar ɗalibai a kwasa-kwasai biyu na Civil Engineering da Mechanical Engineerinng. Jami’ar Khalije Fars na da cibiyoyin bincike guda 9, makarantu 8, sassan kula da al’amuran koyarwa 5, sashen kula da al’adu da ɗalibai, sashen bincike da fasaha, sashen tsarawa da bunƙasawa, da sashen ma’aikata. Yanzu haka ana yin kwasa-kwasai 99 a jami’ar wanda daga cikinsu, 31 na digiri ne, 56 na masters, 13 kuma na PhD.
Saboda yanayin muhallinta da kusancinta da ruwan Tekun Farisa da kuma manyan wuraren mai da iskar gas na yankin Kudancin Pars, ana ɗaukar wannan jami’a a matsayin ginshiƙin ci gaban lardin na Bushehr. Har zuwa farko-farkon shekarar 1996, sunan wannan jami’a ya kasance “Jami’ar Bushehr”, kafin majalisar ƙoli ta sauyin al’adu ta amince da canza mata suna zuwa “”Jami’ar Khalije Fars. Wannan jami’a ita ce jami’ar gwamnati ta farko a lardin Bushehr wadda ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi.
A halin yanzu a jami’ar Khalije Fars akwai ɗalibai 5887 da malamai 221. Alƙaluma sun nuna cewa jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙalolin kimiyya guda 4519 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, kuma ta shirya taruka 8. Baya ga haka, jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙala 1852 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, masu bincike na wannan jami’ar sun wallafa mafiyawan maƙalolinsu da kalmomin “Balaghat” da “Repair and Maintenance” a matsayin muhimman kalmomi
Martabar Jami’a
Jami’ar Khalije Fars ta samu matsayi na 1200-1500 a tsakanin jami’o’in duniya da kuma matsayi 49 a tsakanin jami’o’in ƙasar Iran. A shekarar 2023, jami’ar ta zo a matsayi na 3 wurin samun kuɗin shiga daga masana’antu, matsayi na 5 a daraja a idon duniya, da matsayi na 8 idan an yi la’akari da ɗalibanta na ƙasar waje (inda ta samu matsayi na 21 a shekarar 2023) a tsakanin jami’o’i masu tasowa 39 na ƙasar Iran. Ta kuma samu matsayi na 17 a ɓangaren bincike, matsayi na 25 a taskace bayanai, da matsayi na 35 a ayyukan koyarwa.
Kuɗin makarantar Jami’ar Khalije Fars
Field of Study | Bacholar | Masters | PhD |
---|---|---|---|
Humanities | 375$ | 900$ | 562.50$ |
other fields | 500$ | 1,125$ | 700$ |
Makarantu
School of Literature and Human Sciences
Makarantar Literature and Human Sciences ita ce makaranta ko kwaleji ta 3 a jami’ar Khalije Fars wadda ta fara gudanar da ayyukanta na koyarwa da bincike a shekarar 1995. Da farko kwalejin ta kasance a wani gini a wajen jami’ar kafin a shekarar 2000 a maida ita wurinta na yanzu. Kwalejin na da wuraren koyarwa masu girman murabba’in mita 10,000 a jimilla ɗauke da ɗalibai 4000 masu karanta kwas 24 mabambanta. Kwalejin na karɓar ɗalibai a kwasa-kwasan History, Psychology, Persian Language and Literature, English Language and Literature, Information Science and Knowledge, Arabic Language and Literature.
Faculty of Engineering
Makarantar Engineering ita ce makaranta ta farko ta jami’ar Khalije Fars wadda ta fara aiki a watan October na shekarar 1992 ta hanyar karɓar ɗalibai 34 a fannin Mechanical Engineering, da ɗalibai 35 a kwas ɗin Civil Engineering. Tsawon shekaru ashirin da wani abu da wannan kwalejin ya ɗauka yana aiki, ya kasance ɗaya daga cikin makarantun jami’ar Khalije Fars waɗanda ke sahun gaba kuma waɗanda suka samu nasara sosai a aikinsu. Yanzu haka kwalejin na da ɗalibai 1500 masu karatun kwasa-kwasai 13 mabambanta. Girman wuraren koyarwa na kwalejin ya kai murabba’in ita 10,000 a jimilla. Hakazalika kwalejin na da membobin tsangayar ilimi 37.
Faculty of Intelligent Systems Engineering and Data Science
An assasa wannan kwalejin ne ta hanyar tattaro kwasa-kwasan Electrical Engineering, Computer Engineering daga kwalejin Engineering, da kuma kwasa-kwasan Mathematics da Statistics daga kwalejin Basic Sciences, inda aka haɗe waɗannan kwasa-kwasan a ƙarƙashin wannan kwaleji a shekarar 2019 bisa amincewar manyan jami’ar. Kwalejin na da fannonin Electrical Engineering, Computer Engineering, Mathematics, da Statiscics kuma ya fara ayyukansa ne a shekarar 2020.
Faculty of Science and Nano and Biological Technology
Shi kuma wannan kwalejin da fari sunansa Faculty of Basic Sciences a shekarar 1996 lokacinda aka assasa shi inda ya fara karɓar ɗalibai a fannonin Statistics, Mathematics, Biology, Geophysics, Chemistry, da Physics a matakin digiri, masters, da PhD.
Bisa umarnin da shugabannin makarantar suka bayar na maida kwasa-kwasan Biotech, Marine Environment, da Marine Chemistry daga Faculty of Marine Science and Technology, zuwa wannan kwalejin, shi ne fa aka sauya mata suna zuwa Faculty of Science and Nano and Biological Technology. A lokacin ne su ma kwasa-kwasan Mathematics da Statistics aka cire su daga wannan kwalejin suka koma ƙarƙashin sabon kwaleji mai suna Intelligent Systems Engineering and Data Science.
Faculty of Agriculture and Natural Resources
Wannan kwaleji shi ne na 4 a jami’ar kuma ya fara ayyukansa ne da kwas ɗin Horticultural Science a garin Borazjan. Yanzu haka a kwalejin akwai kwas ɗin karatu 4 a matakin digiri, da 4 a matakin masters, tare da membobin tsangayar ilimi 24.
Faculty of Art and Architecture
Wannan kwalejin ya fara aiki a shekarar 2005 tare da karɓar ɗalibai a matakin digiri na kwas ɗin Architecture. An gina wannan kwalejin ne a cikin salo irin na tarihi na garin Bushehr mai suna “Kuti”, a kusa da ginin “Nozari” mai tsufan tun lokacin daular Qajar. An gina shi ne a wani fili mai girman murabba’in mita 3950, inda ke ɗauke da tsofaffin gine-gine 20 a da. Tsarin ginin wannan jami’a ya haɗa salo biyu na gargajiya da na zamani, da yawan masana na ganin cewa jami’ar tana nuna al’adar tsohon salon gini irin na Bushehr.
Faculty of Petroleum, Gas da Petrochemical Engineering
Wannan makarantar ita ce cibiya mafi muhimmanci a lardin Bushehr ta fuskar kimiyya, koyarwa, da kuma ayyukan bincike. A wannan kwalejin ne ake koyarda keɓantattun fannoni irinsu Petrochemical Engineering da Oil and Gas Engineering da nufin horarda ma’aikatan da ake buƙata wajen sarrafa waɗannan albarkatu na mai da ake da su a lardin. An kafa kwalejin ne a gefen arewa maso gabacin jami’ar Khalije Fars ta garin Bushehr. An fara aikin gina kwalejin ne a shekarar 2003 a wani fili mai girman murabba’in mita 5700 da gine-gine masu girman murabba’in mita 8000, kafin a bunƙasa gine-ginen su kai jimillar murabba’in mita 12000.
Faculty of Marine Science and Technology
Shi kuma wannan kwalejin an buɗe shi ne a shekarar 2011 bisa la’akari da irin rawar da teku ke takawa a wajen bunƙasawa da kawo cigaba a lardin na Bushehr, da hadafin horar da ɗalibai a fannonin da suka shafi ruwa (teku), inda ya fara aikinsa a hukumance ta hanyar karɓar ɗalibai a matakin masters, a kwas ɗin Marine Biotechnology.
A halin yanzu kwalejin na Marine Science yana cikin wani yanki na muhallin kwalejin Basic Science, ɗaliban kwalejin ma suna amfani ne da kayan aikin karatu da na bincike na kwalejin Basic Science. Har ila yau, kwalejin na Marine Science ya ƙunshi kwasa-kwasai mabambanta daga sauran kwalejojin jami’ar. Assasawa da faɗaɗa kwalejin ya faru ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sauran kwalejojin jami’ar, da kuma taimakon yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin jami’ar da wasu muhimman cibiyoyi irinsu cibiyar nazarin teku ta ƙasa, majalisar kula da muhalli, Shilat, ƙungiyar tashohin ruwa, da sauransu.
Faculty of Business
Kwalejin Business ya fara aiki ne a shekarar 2019 ta hanyar ɗunke kwasa-kwasan Business Management, Industrial Mangement, Accounting, da Economics waɗanda ke ƙarƙashin kwalejin Human Science a da, bisa amincewar shugabannin jami’ar. An kafa kwalejin ne da nufin ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙire-ƙirƙire da cigabantar da ɓangaren kasuwanci na jami’ar kasantuwar cewa a baya lardin na Bushehr yana da goshi sosai a fagen kasuwanci, hakan zai iya taimakawa wajen dawo da wannan martaba ta hanyar horar da ƙwararrun masanan kasuwanci da za su bada gudunmawa wajen kawo cigaban ƙasa da duniya baki ɗaya a fagen kasuwanci.
Jam College of Engineering
Wannan kwalejin na Engineering a tsakiyar garin Jam yake, a unguwar Shahrake Pardis kuma ɗaya ne daga cikin kwalejojin wannan jami’a ta Khalije Fars. Kwalejin ya fara aiki ne da kwas biyu na Computer Engineering (software) da Insdustrial Engineering. Zuwa yanzu iya waɗannan kwasa-kwasan biyu ake yi a kwalejin, saidai ana fatan samun ƙarin kwasa-kwasai zuwa gaba. A halin yanzu akwai kimanin ɗalibai 400 da ke karatu a wannan kwaleji, tare da membobin tsangayar ilimi (malamai) guda 8.
Kwasa-Kwasai
- Statistics
- Energy Economy
- Acoounting
- Pure Mathematics
- Chemistry
- Genetics
- Fisheries Science and Engineering
- Industrial Engineering
- Civil Engineering
- Mechanical Engineering
- Computer Engineering
- Petroleum Engineering
- Nanophysics
- Architectural Engineering
- Ship Architectural Engineering – (ship hydromechanics) da sauransu…
Ababen More Rayuwa
- Masaukan ɗalibai maza da na mata
- Self (sabis ɗin abinci)
- Sabis ɗin zirga-zirga zuwa makaranta
- Zauren wasanni
- Masallaci
- Tsarin Intanet
- Ɗakin gwaje-gwaje (laboratory)
- Laburare
Hostel
Na maza
- Wurin kwana na Yadegar 1
- Wurin kwana na Yadegar 2
- Wurin kwana na Yadegar 3
- Wurin kwana na Yadegar 4 (Taleghani)
- Wurin kwana na Yadegar 5 (ɗaliban PhD)
- Wurin kwana na Yadegar 6 (ƙarin jini)
Na mata
- Rukunin Kowsar
- Kowsar 4 (ɗaliban postgraduate)
- Kowsar 5 (Kuti)
Yanayin Wuri
Jami’ar Khalije Fars na nan a garin Bushehr a titin Khajije Fars, Bolvare Mahini. A kusa da jami’ar akwai wurare kamar haka; cibiyar kasuwanci ta Jazire, Arman Hypermarket, Khalije Fars Public Library, Copol Restaurant, da Shoghab Park.
Adireshi: Bushehr, titin Khalije Fars
Shafin jami’a: https://pgu.ac.ir