Jami’ar Ilam ɗaya ce daga jami’o’in gwamnati a garin Ilam wadda ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi ta Iran, kuma ita jami’a mafi ɗaukar hankali a lardin Ilam. Jami’ar Ilam tana ɗaukar hankalin ɗalibai daga ko ina a faɗin duniya.
Gabatarwa
Jami’ar Ilam na ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati mafi inganci a garin Ilam. An assasa wannan jami’a ne a shekarar 1976 a matsayin kwalejin farko ta Animal Husbandry mai zaman kanta a ƙarƙashin Jami’ar Razi ta Kermanshah, kafin ta fara cin gashin kanta a shekarar 1992.
Jami’ar na karɓar ɗalibai a kwasa-kwasai guda 120 a duka matakan karatu, sannan tana ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati da ake ji da su. A wannan rubutun za mu yi ƙoƙarin kawo muku bayanai don ku ƙara samun masaniya a kan wannan jami’a ta Ilam.
A halin yanzu akwai kimanin ɗalibai 7000 da malamai 199 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi 5712 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan ta wallafa mujalla 5 na musamman, kuma zuwa yanzu ta shirya taruka 4. Har ila yau, jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙala 4380 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, masu bincike na wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kalmomin “Nanoparticles” da “Pea” a matsayin muhimman kalmomi.
Martabar Jami’a
A bayanin da tsarin ranking na Webometrics ya fitar a watan July na shekarar 2021, Jami’ar Ilam ta samu matsayi na 3042 a tsakanin jami’o’in duniya, da kuma matsayi na 76 a tsakanin cibiyoyin koyarwa na Iran waɗanda suka haɗa da jami’o’i gama gari, jami’o’in fasaha, jami’o’i masu zaman kansu, cibiyoyin bincike, da jami’o’in likitanci.
Kuɗin makarantar Jami’ar Ilam
Degree | Annual Tuition |
---|---|
Humanities Bachelor | 480$ |
Science Bachelor | 580$ |
Master Humanities | 900$ |
Master Science | 1,100$ |
Ph.D. Humanities | 1,160$ |
Ph.D. Science | 1,560$ |
Makarantu
- Faculty of Literature and Humanities
- School of Theology and Islamic Studies
- School of Paramedicine
- School of Basic Sciences
- School of Technical Engineering
- Facuty of Agriculture
- School of Oil and Gas
Kwasa-Kwasai
- Electrical Engineering
- Renewable Energy Engineering
- Architectural Engineering
- Architecture and Energy
- Geography and Urban Planning – urban planning
- Computer Engineering – software
- Computer Engineering – algorithms and calculations
- Chemical Engineering
- Petroleum – oil
- Chemical Engineering – separation processes
- Civil Engineering
- Civil Engineering – structure
- Mechanical Engineering
- Associate of Veterinary Medicine
- Continuous Laboratory Science
- Discontinuous Laboratory Sciences
- Food Hygiene
- Science and Engineering of Food Industries
- Veterinary Bacteriology
- Veterinary Histology
- Accounting
- Theoretical Economics
- Commercial Economy
- Economic Sciences
- Energy Economy
- Economic Development
- Business Management
- Organizational Behavior Management
- Management – human resource development trend
- Management – transformation orientation
- Marketing Management
- Management – strategic
- Business Management – entrepreneurship
- Persian Language and Literature
- Arabic Language and Literature
- English Language and Literature
- General Linguistics
- Teaching English
- Sociology – research
- Law
- History
- History of Shiism
- Cultural Studies
- Iraqi Studies
- Sports Science
- Orientation Sports Management (strategic management in sports organizations)
- Animal Science Engineering
- Animal Science – Poultry nutrition
- Animal Science – animal nutrition
- Animal Science – Livestock and poultry physiology
- Horticultural Science Engineering
- Science and Engineering of Horticulture-fruit trees
- Horticultural Science and Engineering – vegetables
- Horticultural Science and Engineering – medicinal plants
- Horticultural Science and Engineering – ornamental plants
- Physiology and Improvement of Fruit Trees
- Production Engineering and Plant Genetics
- Agrotechnology – Physiology of Crops
- Agro Technology – ecology of agricultural plants
- Genetics and Plant Breeding
- Rural Development
- Entrepreneurship – new business
- Water Engineering
- Engineering of Water Structures
- Soil Resource Management (soil resource trend and land evaluation)
- Fertility Management and Soil Biotechnology (soil biotechnology trend)
- Nature Engineering
- Watershed Science and Engineering
- Desert Management and Control
- Military Engineering
- Forest Science and Technology Engineering
- Forest Management
- Forest Biology
- Biosystem Mechanical Engineering
- Biosystem Mechanical Engineering (design and construction)
- Biosystem Mechanical Engineering (renewable energies)
- Biosystem Mechanical Engineering (post-harvest technology)
- Agricultural Mechanization Engineering (systems management and analysis)
- Agricultural Mechanization Engineering (Energy)
- Agricultural Mechanization Engineering (recycling and waste management)
- Medicinal Plant
- Plant Pathology
- Islamic Philosophy and Theology
- Islamic Jurisprudence and Fundamentals of Law
- Quran and Hadith Sciences
- Biotechnology
- Microbiology (pathogenic microbes)
- Systematic Plant Sciences and Ecology
- Microbiology (pathogenic microbes – cellular and molecular)
- Pure Chemistry
- Mineral Chemistry
- Organic Chemistry
- Analytical Chemistry
- Physical Chemistry
Ababen More Rayuwa
- Jami’ar Ilam tana da laburare mai girman murabba’in mita 600 ɗauke da kwafin litattafai kusan7000.
- Muhallin da jami’ar Ilam take muhalli ne mai kyau saboda akwai yiwuwar zuwa wurin cikin sauƙi daga wurare da dama na garin Ilam, har ma da wasu garuruwa na kusa da Ilam ta hanyar amfani da motar makaranta.
- Jami’ar na da ɗakin gwaje-gwaje na Biochemistry, Parasitology, Microbiology, Laboratory for Preparation of Microscopic Sections, da Research Laboratory.
Hostel
Mabambantan kayan aikinta na daga cikin muhimman abubuwan da ke gamsar da ɗalibai da kuma jan hankalin sabbin ɗalibai zuwa jami’ar. Ɗaya daga cikin kayan aikin da jami’ar Ilam ta tanadar wa ɗalibanta shi ne wuraren kwana wato hostel na ɗalibai maza da na mata, da kuma ɗalibai masu iyali. Maƙurar tsawon lokacin da ɗaliban Digiri za su iya amfani da hostel shekara 4 ne, ɗaliban Associate Degree kuma shekara 2, ɗaliban Masters shekara 2, ɗaliban PhD kuma shekara 4. Jerin Wuraren kwanan Jami’ar Ilam:
- Wurin kwana na Khalil Ja’afari
- Wurin kwana na Nizamul Din Ansari
- Wurin kwana na Ghadir
- Wurin kwana na Danesh
- Wurin kwana na Ikhtiyar Zadeh
- Wurin kwana na Rezayi Nejad
- Wurin kwana na Andishe
- Wurin kwana na Motahhari
- Wurin kwana na Bintul Huda
- Wurin kwana na Vermaziar
Daga cikin abubuwanda waɗannan hostel suka shahara da su akwai laburare masu ɗauke da taken litattafai 80,000 na farsi da latin, Thesis 2000 na ɗalibai, wallafaffun mujalloli, da sansanonin bayanai. Dukan ɗalibai za su iya amfani da litattafan da suke buƙata a cikin laburaren ko su yi rizab ta online. Baya ga haka, ɗalibai za su iya muɗali’ar shafi 20 na thesis ɗin mabambantan kwasa-kwasai don gudanar da ayyukansu na bincike.
Yanayin Wuri
Jami’ar Ilam na nan a titin Daneshjo, Bolvare Pojohesh. Tashar bus mafi kusa da jami’ar ita ce tashar bus ta jami’ar Ilam, hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga ga ɗalibai da ma’aikatan da ba su da abun hawa.
Adireshi: Garin Ilam, Bolvare Daneshjo, Bolvare Pajohesh.
Shafin jami’a: https://www.ilam.ac.ir