[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Kurdistan University of Medical Sciences

Karatu a Kurdistan University of Medical Sciences

Loading

Kurdistan University of Medical Sciences wata cibiyar koyarwa ce, mai gudanar da ayyukan jinya da kiwon lafiya a garin Sanandaj, lardin Kurdistan. A wannan maƙala, zamuyi magana akan karatu a Kurdistan University of Medical Sciences da sauran bayanan da suka shafi wannan makaranta, wanda hakan zai taimaka muku wurin yanke shawara da kuma zaɓen makaranta.

Gabatarwa

Har zuwa kafin juyin musulunci na Iran, babu wata makaranta ko jami’ar karatun likitanci a Kurdistan. A shekarar 1986 aka assasa Kurdistan University of Medical Sciences inda ta fara aiki a iya matakin Associate Degree kuma da kwasa-kwasan Nursing da Laboratory Sciences .
Wannan jami’a tana da kimanin ɗalibai 2551, malamai 252, da mambobin kwamitin ilimi 296. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta samu nasarar wallafa maƙalar ilimi guda 951 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida [wanda suka haɗa da mujalla 475 da maƙalar taro guda 476], hakazalika ta wallafa karɓaɓɓun maƙaloli guda 2694 a matakin ƙasa da ƙasa. Kurdisatan University of Medical Sciences ta mallaki mujalla 5 na musamman.

Martabar Jami’a

Tsarin ranking na Times a kowace shekara yana martaba cibiyoyin koyarwa bisa la’akari da abubuwa 4; bincike, kulawa, cigaba, da kuma karatu. Kurdistan University of Medical Sciences ta yi nasarar samun mastayi na 101 – 200 a fannin lafiya da warkarwa, matsayi na 101 – 200 a fannin ingacin karatu, matsayi na 600 – 401 a fagen daidaita jinsi, da kuma matsayi na 801 – 1000 a fagen musharaka cikin tsarin tabbatar da cigaba mai ɗorewa a matakin ƙasa da ƙasa.

Karatu a Kurdistan University of Medical SciencesMakarantu

_School of Medicine
_School of Dentistry
_Faculty of Paramedicine
_Faculty of Health
_School of Nursing and Midwifery
_Saqaz Higher Complex

Jadawalin Kuɗin Makarantar Kurdistan University of Medical Sciences

Kwasa-Kwasai

_Medicine
_Dentistry
_Surgery Room
_General Hygiene
_Nursing
_Radiation Therapy Technology
_Radiology Technology
_Laboratory Sciences
_Midwifery
_Environmental Health Engineering
_General Medicine
_Immunology
_Bacteriology
_Physiology
_Anatomical Sciences
_Epidemology
_Clinical Biochemistry
_Molecular Medicine
_Emergency Medicine
_Anesthesia
_Children
_Internal
_General Surgery
_Obstetrics and Gynecology
_Psychiatry
_Special Care Nursing
_Medical Emergency
_ Emergency Nnursing
_Radiology
_Da sauransu…
Domin samun cikakken bayani akan kwas ɗinku da matakin karatu, ku sauke wannan fayil.

Kwasa-Kwasan Kurdistan University of Medical Sciences

Kwasa-Kwasan Kurdistan University of Medical SciencesAsibitoci

_Kausar Sanandaj Medical, Educational and Therapeutic Center
_Sanandaj Mission Medical, Educational and Therapeutic Center
_Tawheed Sanandaj Medical, Educational and Therapeutic Center
_Quds Medical, Educational and Therapeutic Center
_Imam Khomeini Hospital, Saqez
_Dehgolan Martyrs Hospital
_Imam Khomeini Diwandare Hospital
_Salahuddin Ayubi Baneh Hospital
_Imam Hussain (AS) Hospital, Bijar
_Shahid Chamran Hospital, Sarovabad
_Boali Hospital, Marivan
_Sina Hospital, Kamiyaran
_Fajr Marivan Hospital
_Shahid Beheshti Hospital Qorveh
_Razi Baneh Hospital
_Saqez Healing Hospital
_Sanandaj Special Clinic

Cibiyoyin Bincike

_Cell and Molecular Research Center
_Environmental Health Research Center
_Research Center for Social Factors Affecting Health
_Gastroenterology and Liver Research Center
_Neuroscience Research Center
_Cancer and Immunology Research Center
_Zoonosis Research Center
_Lung and Allergy Research Center
_Spiritual Health Research Center
_Clinical Care Research Center

Ɗakunan Karatu

_Laburaren Asibitin Kausar
_Laburaren Asibitin Ba’ath
_Laburaren Asibitin Tawheed
_Laburaren Asibitin Quds
_Laburaren Faculty of Medicine
_Laburaren Faculty of Dentistry
_Laburaren Faculty of Dentistry
_Laburaren Faculty of Nursing and Midwifery
_Laburaren Faculty of Health
_Babban Laburare [mai ɗauke da sama da kwafi dubu ɗari na littafai, projects, mujallu, da maƙaloli]
_Digital Library

Abubuwan Alfahari

_Kammala duka matakai uku na tiyatar Cervical Disc Surgery cikin nasara karon farko a Kurdistan, wanda Dr. Shokrallah Zandi, ƙwararren likitan fiɗar ƙwaƙwalwa da spinal cord kuma Neurosurgeon yayi (Daga Department of Surgery and Anesthesia).
_ Aiwatar da tiyatar kansar harshe ta hanyar amfani da na’urar Harmonic Ultrasound, karon farko a Kurdistan wanda Dr. Hosein Moiri, gwani a tiyatar kansa yayi.
_ Aiwatar da tiyatar farko ta kansar mama a Kurdistan ta hanyar amfani da na’urar Gamma Probe, wanda Dr. Hosein Moiri (gwani a tiyatar kansa) yayi.
_Ɗaliban likitanci masu hazaƙa sun samu nasara a jarabawar residency karo na 47

Ababen More Rayuwa

Wurin Kwana: Kurdistan Univerity of Medical Sciences tana da hostel guda 13 wanda ciki akwai hostel 2 na masu iyali (ɗaya na titin Adan kuma yanada sassa 8, ɗayan kuma yana da sassa 32 kuma yana unguwar Baharan, a halin yanzu akwai ɗaliban wannan jami’a su 40 da suke zaune a waɗannan sassan tare da iyalansu), hostel 2 domin ɗalibai maza wɗanda aka karɓa haya daga Jahad Daneshgahi, wanda suna ƙarƙashin kulawar jami’ar kai tsaye, hakazalika duka ayyukkan tafiyarda waɗannan wuraren suna hannun jami’a. Ɗaya daga cikin wuraren kwanan wannan jami’ar kuma ya keɓanci ɗaliban da ke zuwa daurori na musamman. Hostel 5 sun keɓanci ɗalibai maza ne, kuma duka suna wajen makarantar. Sauran 5 ɗin kuma da suke na ɗalibai mata ne, 4 suna cikin makarantar 1 kuma yana waje. A halin yanzu akwai ɗalibai maza 600, ɗalibai mata 800 da kuma ɗalibai magidanta 40 da ke zaune a waɗannan hostel. Batun kuɗin hostel kuma, jami’a bata karɓar kuɗi daga hannun ɗalibai sai sun kammala karatunsu, bayan kammalawa kuma ana biyan wannan kuɗin daga asusun tallafin ɗalibai ne, su kuma ɗaliban su biya a hankali (kamar bashi).

Kayan aikin Kurdistan University of Medical SciencesYanayin Wuri

Kurdistan University of Medical Sciences tana cikin garin Sanandaj a titin Pasdaran, gaba da titin Shohadaye Niroye Intizami. Jami’ar tana kusa da wurare kamar; Asibitin Kausar,  Faculty of Dentistry,  Bu Ali Sina Park,  Tashar Bus ta titin Pasdaran,  Dental Clinic, Sanandaj Jahangardi Hotel, Shadi Hotel, da kuma gidan mai na Naseri Baharan.

Adireshin Kurdistan University of Medical Sciences

Adireshi Kurdistan University of Medical Sciences, Titin Abidar.


Tambayoyin da ake yawan yi

  1. Wasu takardu ake buƙata don yin rajista a wannan jami’a?
    Passport, Hoto, Scripts, Certificate, CV, Motivation Letter, Recommendation Letter.
  2. Ko ɗaliban Iraq zasu iya yin transfa a wannan jami’ar?
    Eh, ɗaliban Iraq zasu iya yin transfa zuwa ƙasarsu bayan sun kammala semester ta biyu.

[neshan-map id=”10″]

یک پاسخ بنویسید