[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Damghan University

Loading

Jami’ar Damghan na ɗaya daga cikin makarantun gwamnati a ƙasar Iran wadda ke arewa maso yammacin garin Damghan, lardin Semnan. Ita ma Jami’ar Semnan a wannan lardi na Semnan take. Akwai fa’idodi da yawa a cikin karatu a wannan gari na Damghan wanda ɗaya ne daga cikin tsofaffin garuruwa masu ɗimbin tarihi a Iran. Akwai yanayi mai kyau na ɗabi’a a wannan gari, wanda yana jan hankalin maziyarta masu yawon buɗe ido. Kaɗan a wajen garin na Damghan ta yamma akwai dazuzzuka da duwatsu, ta kudu kuma akwai hamada da yashi.

Gabatarwa

Kusan duka abubuwan da wannan jami’a take da su sun tattaru ne a cikin harabar jami’ar da kuma wasu sassan garin na Damghan ta yadda ɗalibai za su iya amfani da su cikin sauƙi. Hakazalika mafi yawan gine-ginen jami’ar da wuraren kwananta sabbin ginawa ne kuma masu inganci. Daga cikin fannonin da ake yi a wannan jami’a ta Damghan akwai Basic Sciences, Engineering and Tech, da Arts and Social Sciences.

A halin yanzu akwai ɗalibai 5732 da malamai 137 a jami’ar. Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu jami’ar Damghan ta wallafa maƙalar kimiyya 2070 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, maƙala 1922 a matakin ƙasa da ƙasa, da kuma mujalla 6 na musamman. Jami’ar ta mallaki lambar yabo, sannan kuma ta shirya taruka 6 zuwa yanzu. A shekarar 2023 masu bincike na wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kalmomin “analytical methods” da “descriptive” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.

Karatu a Jami'ar Damghan

Martabar Jami’a

A sabon sakamakon da tsarin ranking na “Nature Index” ya fitar, Jami’ar Damghan ta zo a matsayi na 10 a jami’o’in Iran. Wannan tsarin yana martaba jami’o’in duniya ne bisa la’akari da ingancin ayyukansu na bincike a fannin basic sciences a kan maudu’an Biology, Chemistry, Physics, Geology, da Environment.

Tsarin ranking na TIMES na ɗaya daha cikin fitattun tsarukan ranking na duniya wanda ke martaba jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na duniya a kowace shekara . A sakamakon da tsarin ya fitar na shekarar 2022 biyu ga watan September, jami’ar Damghan a karon farko ta samu shiga jerin fitattun jami’o’in duniya inda ta zo a matsayi na 1201 – 1662 a duniya, a tsakanin jami’o’in Iran 58 kuma ta samu matsayi na 44.

Kuɗin makarantar Jami’ar Damghan

fieldAnnual tuition in dollars
Masters Humanities200$
Masters other fields250$
PhD325$

Makarantu

Faculty of Mathematics and Computer Science

Da fari wannan kwaleji yana ƙarƙashin kwalejin Basic Science ne a matsayin department ɗin mathematics inda ya fara aiki a shekarar 1994 da kwas ɗin applied mathematics da mathematics. A shekarar 1999 ne aka fara kwas ɗin pure mathematics a wannan kwalejin. Kwalejin na da professor 1, associate professor 6, assistant professor 17, da supervisor 2.

Faculty of Biology

Tana ɗaya daga cikin makarantu mafi daɗewa na jami’ar Damghan, wadda ta fara aiki ne a shekarar 2007 a fannoni 3 na Plant Science, General ‌Biology, da Molecular Cell.

School of Chemistry

Sashen chemistry na wannan jami’ar ya fara aiki da kwas ɗin pure chemistry a shekarar 1994. Yanzu haka a wannan kwalejin ana yin kwas 2 a matakin digiri; pure chemistry da applied chemistry. Akwai associate professor 9, assistant professor 10, da professor 4 a kwalejin na chemistry.

Faculty of Earth Sciences

Wannan kwalejin ya kasance shi ne department na farko a jami’ar kuma ya fara aiki ne da ɗalibai 35 da sunan department of earth sciences, a shekarar 1992. Ya fara ne da kwas ɗin Pure Geology kafin a ƙara da kwas ɗin Applied Geology a shekarar 2008, daga nan kuma aka fara karɓar ɗaliban Geomorphology. Yanzu haka wannan kwalejin na da assistant professor 1, associate professor 3, da ɗalibai 230 a matakin digiri, 35 a matakin masters.

Faculty of Technical Engineering

A farkon shekarar 2010 ne bisa amincewar ofishin bunƙasa karatun gaba da sakandare, aka samar da wannan kwalejin na Technical Engineering. Ofishin ya bada lasisin buɗa fannonin software engineering da industrial engineering bisa la’akari da yanayin jami’ar, inda aka fara karɓar ɗalibai a zangon karatu na biyu na shekarar 2011/2012. Yanzu haka akwai malamai masu darajar associate professor guda 5, assistant professor 23, da malamai 5.

Faculty of Physics

Wannan kwalejin ya fara aiki ne a shekarar 1996. Yanzu haka a kwalejin ana yin kwas guda biyu a matakin digiri; Physics da Engineering Physics, kwas 5 a matakin masters, da kwas 3 a PhD. Kwalejin na da assistant professor 15, associate professor 5, da professor 2.

Faculty of Art

Shi kuma wannan kwalejin na art ya fara ayyukansa ne a shekarar 2011 da fannoni biyu na Television and Digital Arts da kuma Dramatic Literature. Kwalejin na da workshop guda 9 kamar haka: Photography Workshop, Show Workshop (guda biyu), Graphic Workshop, 2D Animation Workshop, Computer Site, Puppet Animation Workshop, General Design Workshop, da kuma Animation Design Workshop.

Faculty of Humanities

Shi kuma wannan kwalejin ya fara aiki ne a shekarar 2013 da kwas ɗin Jurisprudence (fiqh) da Law a matakin masters. Daga baya a shekarar 2016 aka fara kwas ɗin sport sciences, geography, da law a matakin digiri, a matakin masters kuma aka ƙara da kwas ɗin Arabic Language Translation, aka kuma ƙara kwas ɗin English Language da Economics a shekarar 2017.

Karatu a Jami'ar DamghanKwasa-Kwasai

  • Geography
  • Geology
  • Petrology
  • Stratigraphy and Paleontology
  • Geology and Tectonics
  • Geological Engineering
  • Economic Geology
  • Mineralogy and Industrial Stones
  • ریاضی‌محض
  • Applied Mathematics
  • Computer Science
  • Pure Chemistry
  • Applied Chemistry
  • Analytical Chemistry
  • Physical Chemistry
  • Organic Chemistry
  • Mineral Chemistry
  • Applied Chemistry
  • Degradative Polymer Chemistry
  • Physical Chemistry
  • Organic Chemistry
  • Mineral Chemistry
  • Physics
  • Engineering Physics
  • Solid Mode
  • Astronomy and Astrophysics
  • Nuclear
  • Gravity and the Universe of Dense Matter (solid state)
  • Nuclear Physics and Nanophysics
  • Animal Biology
  • Cellular and Molecular Biology
  • Biology
  • Plant Science
  • Plant Physiology
  • Systematic Ecology
  • Biogenesis
  • Animal Physiology
  • Biochemistry
  • Animal Physiology
  • Civil Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Computer Engineering
  • Industrial Engineering
  • Electrical Engineering
  • Chemical Engineering
  • Television and Digital Arts
  • Sport Sciences
  • Geography
  • Law
  • Arabic Language Translator
  • English Language
  • Economic
  • Dramatic Literature

Ababen More Rayuwa

  • Babban Laburaren Jami’ar
  • Student Centers
  • Specialized Laboratories
  • Counseling Center
  • Department of Physical Education
  • Scientific Community

Karatu a Jami'ar Damghan

Wuraren kwana

  • Wurin kwana na Abuzar
  • Wurin kwana na Golestan
  • Wurin kwanan malamai
  • Wurin kwanan ɗalibai mata
  • Wurin kwana na Mohammad

Yanayin Wuri

Jami’ar Damghan na nan a unguwar Bustan ta garin Damghan, a titin Daneshgah. A kusa da jami’ar akwai wurare kamar Inqilab CNG Stand, Mumtaz Supermarket, Bustane Daneshju, Daneshju Parking Suite, da ofishin mataimakin shugaban Damghan Municipality City Services. Tashar bus mafi kusa da jami’ar ita ce tashar bus ta Karkonan, hakan ya samar da sauƙin zirga-zirga ga ɗalibai da ma’aikata marasa abun hawa.

Adireshi: Damghan, Bustan, titin Daneshga

Shafin jami’a: https://du.ac.ir

 

یک پاسخ بنویسید