[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Razi University

Karatu a Razi University

Loading

Jami’ar Razi wata jami’a ce ta gwamnati a garin Kermanshah. Jami’ar ta fara aiki ne da sunan “Kwalejin Kimiyya ta Kermanshah” a shekarar 1973 kafin daga bisani a canja mata suna zuwa “Jami’ar Razi” a shekarar 1975. Karatu a wannan jami’a ta Razi na da alfanu sosai, ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

Jami’ar Razi ta fara aiki ne a watan January na shekarar 1973 da sunan “KwalejinKimiyya”da taimakon wasu daga cikin malaman jami’a irinsu Fareidon Motamed Vazeri da Abdul Ali Gouya, inda ta karɓi ɗalibai 200 a farkon shekarar karatu ta 1973/1974 a fannoni 4 na Physics, Chemistry, Biology, da Mathematics. A shekarar 1975 ne aka canja sunan wannan cibiyar zuwa “Jami’ar Razi”.

Ita dai wannan jami’a ta Razi jami’a ce ta gwamnati a garin Kermanshah, lardin Kermanshah assasawar shekarar 1973 kamar yadda muka ambata a baya. A halin yanzu akwai ɗalibai 13887 da kuma malamai 1351 a jami’ar. Bayanai sun nuna cewa jami’ar Razi ta wallafa maƙalolin kimiyya 13094 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo, kana ta wallafa mujalla 15 na musamman, kuma ta shirya taruka 18 zuwa yanzu. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙala 7296 a matakin ƙasa da ƙasa. Za ku iya samun ƙarin bayanai game da jami’ar Razi a ƙasa. Masu bincike na wannan jami’ar sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu na shekarar 2023 ɗauke da kalmomin “Kermanshah” da “Nokhod” a matsayin muhimman kamlomi.

Karatu a Razi University

Martabar Jami’a

A ranking na shekarar 2023, jami’ar Razi ta yi nasarar samun ci gaba da zango 200 daga matsayinta na shekarar 2022, inda ta samu matsayi na 1000-1200 a tsakanin jami’o’in duniya, da kuma matsayi na 8 a tsakanin jami’o’in ƙasar Iran. Jami’ar Razi ta samu matsayi na 1200 zuwa sama ne a shekarar 2022 a tsarin ranking na TIMES. Ma’aunan martaba jami’o’i na tsarin TIMES sun haɗa da: Ayyukan koyarwa (maki 29.5), Ayyukan Bincike (maki 29), Taskace bayanai (maki 30), daraja a idon duniya (maki 7.5), kuɗin shiga daga masana’antu (maki 4). Jami’ar Razi ta samu matsayi na 812 a ayyukan koyarwa, matsayi na 1202 a ayyukan bincike, matsayi na 1158 a ingancin ayyukan bincike, matsayi na 1637 a idon duniya, da kuma matsayi na 1010 a kuɗin shiga.

Kuɗin makarantar jami’ar Razi

TitleBacholarMastersPhD

Makarantu

  • School of Literature
  • School of Physical Education
  • School of Chemistry
  • School of Science
  • School of Social Sciences
  • Technical College
  • Faculty of Agricultural Sciences and Engineering
  • Faculty of Agriculture
  • School of Veterinary Medicine
  • Javanroud School of Management and Accounting
  • West Islamabad College of Engineering and Technology
  • Sanghar School of Agriculture

School of Literature

An kafa wannan kwalejin ne a shekarar 1988 a wani muhalli wanda yanzu ya koma kwalejin Social Sciences, inda ake koyar da yaren farsi da adabinsa. Bayan ƙaruwar sassan koyarwa da bunƙasa kwalejin, tare da ɓamɓare kwalejin literature daga kwalejin social sciences a shekarar 2007, an maida kwalejin na literature zuwa sabon muhalli a campus ɗin Taq-e Bostan.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Department of Theology
  • English Department
  • Department of Geography
  • Department of Persian Language and Literature
  • Arabic Literature Department
  • Department of Islamic Studies
  • Department of Law, Historical Sciences and Archaeology

School of Physical Education

An buɗe department ɗin Physical Education da Sport Sciences a shekarar 1994 a cikin kwalejin Literature. A watan February na shekarar 1998 ne aka raba department ɗin da kwalejin literature aka maida shi ƙarƙashin kwalejin physical education. Daga shekarar 2003 kuma aka maida shi a campus ɗin jami’ar Razi inda ya bar ƙarƙashin kowace kwaleji.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Sports Department

School of Chemistry

Department ɗin chemistry na jami’ar Razi ya fara aiki ne a shekarar 1974 a ƙarƙashin kwalejin Sciences a matakin digiri.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Organic Chemistry
  • Applied Chemistry
  • Analytical Chemistry
  • Mineral Chemistry
  • Physical Chemistry
  • Nanoscience and Technology

School of Science

Wannan kwalejin ya fara aiki ne a shekarar 1972 tare da department ɗin mathematics, physics, da biology, kafin daga bisani aka ƙara deptarment ɗin statistics a shekarar 1995.

  • Sassan koyarwa na wannan kwaleji:
  • Statistics
  • Mathematics
  • Bilogy
  • Physics

Karatu a Razi University

School of Social Sciences

Bayan da aka raba kwalejin literature da na social sciences a shekarar 2007, yanzu kwalejin social sciences na nan a wani muhalli mai girman kusan murabba’in mita 30,000 a titin Shahid Beheshti inda yake ci gaba da gudanar da ayyukansa.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Political Science
  • Economic
  • Social Sciences
  • Consultation
  • Information Science and Epistemology
  • Psychology
  • Management and Entrepreneurship
  • Acoounting

Technical College

An fara aikin ginin kwalejin Technical Engineerig a shekarar 1989 inda ya fara aiki a shekarar 1992.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Department of Electrical Engineering
  • Department of Chemical Engineering
  • Department of Civil Engineering
  • Department of Computer Engineering
  • Department of Mechanical Engineering
  • Department of Architectural Engineering
  • Department of Materials and Textile Engineering

Agriculture and Natural Resources Campus

Kwalejin Agriculture ya fara aiki ne a shekarar 1982 a matsayin cibiyar koyarwa ta Agriculture. Bayan bunƙasa departments da kwasa-kwasan karatu, shi ma aka maida shi kwaleji mai zaman kansa kafin a maida ta campus guda shekarar 2011, ɗauke da makarantu 3 (School of Agricultural Science and Engineering, Faculty of Veterinary Medicine, da Faculty of Agriculture).

Faculty of Agricultural Sciences and Engineering

  • Department of Animal Science
  • Department of Water Engineering
  • Department of Production Engineering and Plant Genetics

Facuty of Agriculture

  • Department of Promotion Engineering
  • Department of Natural Resources
  • Department of Soil Science and Engineering
  • Department of Herbal Medicine
  • Department of Biosystem Mechanics

School of Veterinary Medicine

  • Department of Basic Sciences and Pathobiology
  • Department of Clinical Sciences

Javanroud School of Management and Accounting

Wannan kwalejin ya fara aiki ne a watan September na shekarar 2012.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Department of Business Administration
  • Department of Financial Management
  • Department of Accounting

West Islamabad College of Engineering and Technology

Wannan kwalejin a garin Islamabad ta yamma yake, kuma ya fara aiki ne a shekarar 2011.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Department of Industries
  • Department of Computer
  • Department of Civil

Sanghar School of Agriculture

Wannan kwalejin ya fara aiki ne a watan September na shekarar 2013.

Sassan koyarwa na wannan kwaleji:

  • Department of Biosystem Mechanics
  • Department of Agricultural Mechanization
  • Department of Food Industry Machines

Cibiyoyin bincike da ɗakunan gwaje-gwaje

  • University Research Institute
  • Enterprise Architecture Laboratory
  • Architectural Research Institute
  • APA Center
  • Razi Language Center
  • RULPT University Language Test Center
  • Cloud Computing Research Center
  • Environmental Research Center
  • Telecommunications Research Center
  • Chemical Engineering Advanced Research Institute

Karatu a Razi University

Ababen More Rayuwa

Jami’ar Razi ta yi tanadin dukan abubuwan buƙatu domin ɗalibanta, abubuwa kamar; wurin cin abinci, sansanin bada agajin gaggawa, cibiyra sayar da littafai, clinic, wallafe-wallafen jami’a, masauki, sashen motsa jiki da asusun jin daɗin ɗalibai da ma’aikata, da sauransu. Jami’ar Razi na da hostel guda 7 na ɗalibanta maza da na mata.

Babban laburaren jami’ar Razi ta Kermanshah shi ne laburare mafi girma na yankin gabacin ƙasar Iran a halin yanzu, wanda yana ɗauke da kimanin kwafin littafai 50,000. Hakazalika yana da ƙananan laburare guda 5 a ƙarƙashinsa waɗanda ke baje a kwalejojin jami’ar.

  • Laburaren kwalejin Literature
  • Laburaren kwalejin Physical Education
  • Laburaren kwalejin Veterinary Medicine
  • Laburaren kwalejin Agriculture
  • Laburaren kwalejin Social Sciences

Yanayin Wuri

Jami’ar Razi ta garin Kermanshah na nan a unguwar Taq-e Bostan, titin Daneshga. Jami’ar na kusa da wurare kamar makarantar sakandare ta maza ta Kermanshah, Pirayishe Vahid, Bostan Specialized Clinic, Danesjo Park, da sashen abinci da magunguna na Kermanshah University of Medical Sciences.

Adireshi:Kermanshah, Taqe-Bostan, titin Daneshga, Razi University.

Shafin Jami’a: https://razi.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *