Karatu a Iran: Damammakin Musamman ga Ɗaliban Ƙasashen Waje
Ko kuna sha’awar yin karatu a Iran? Ku gina gobenku a ɗaya daga cikin wuraren karatu mafi inganci a duniya ta hanyar binciko damarmakin karatu na musamman tare da al’dau masu yawa. Cikakken bayani game da ƙa’idojin samun admission, scholarship, da yanayin rayuwar ɗalibai a ƙasar Iran, ga ɗaliban ƙasashen waje.
Karatu a Iran na ba wa ɗaliban ƙasashen waje wata gagarumar dama ta musamman mai cike da ban sha’awa. Duba da tarihinta mai zurfi da bambancin al’adunta, ƙasar Iran tana ƙara shiga idanu a matsayin muhimmiyar cibiyar karatu. Ƙasar na ba wa ɗalibai damar bunƙasa iliminsu tare da al’adu, wanda hakan zai iya yin babban tasiri a rayuwarsu da kuma sana’o’insu.
Bambancin Al’adu
Iran, kasancewarta ƙasa mai mabambantan ƙabilu, wuri ne da ya tattara al’adu da yaruka daban-daban a wuri ɗaya. Tun daga kan Kurdawa, Farisawa, da Baluchawa, kowace ƙabila tana da nata halaye keɓantattu. Ɗalibai za su iya musharaka a taruka da bukukuwan gargajiya, domin sabawa da al’adun kowane yanki da kuma ƙara tajarubar rayuwa ta hanyar mu’amalantar al’adunsu.
Manyan Jami’o’i
Iran na da sanannun jami’o’i a duniya irin su Tehran University, Sharif University of Technology, da Amirkabir University of Technology. Waɗannan jami’o’in na da ingantaccen tsarin koyarwa da kayan aiki na zamani don amfanin ɗalibai a mabamban fannonin karatu. Hakazalika, da yawan waɗannan jami’o’in na Iran suna musharaka a ayyukan bincike na ƙasa da ƙasa.
Mabambantan Fannonin Karatu a Iran
Iran na ba ma ɗalibai damar karanta fannoni daban-daban na ilimi. Tun daga kan medicine da engineering, har zuwa art da social sciences. Wannan bambancin kan ba ma ɗalibai damar zaɓen kwas ɗin da ya dace da manufofinsu na rayuwa da sana’o’i.
Sauƙin Tsadar Rayuwa a Iran
Daga cikin manyan amfanukan karatu a Iran shi ne sauƙin rayuwa. Kuɗin muhalli, abinci, da zirga-zirga na da sauƙi sosai idan aka kwatanta da sauran manyan ƙasashe, musamman ƙasashen yamma. Wannan kan taimaka ma ɗalibai su yi rayuwa a yalwace amma a cikin tattali.
Farashin rayuwa ga ɗaliban ƙasashen waje kan iya bambanta bisa la’akari da gari, yanayin rayuwar su kansu ɗaliban, da kuma makarantunsu. Amma a ƙiyasi, ga matsakaicin farashin da zai ishi mutum rayuwa a wata ɗaya a lissafin dalar Amurka kamar haka:
Kuɗin | Ƙiyasin farashi (Dala/wata ɗaya) |
---|---|
Hayar Gida(ɗakin kwana 1) | 150 – 300 USD |
Abinci (A wurare masu sauƙin kuɗi) | 50 – 100 USD |
Sayayya (sayayyar wata 1) | 100 – 150 USD |
Zirga-Zirga a ababen hawa na gama-gari | 10 – 20 USD |
Kuɗin data da katin waya | 10 – 20 USD |
Kiwon lafiya da kuɗin magani | 10 – 30 USD |
Nishaɗi da shaƙatawa | 20 – 50 USD |
Jimilla | 350 – 650 USD |
Abun Lura:
- Haya: Akwai bambanci tsakanin kuɗin haya a garuruwa daban-daban, ya danganta da garin da za a biya hayar (a manyan birane irin Tehran kuɗin haya ya fi tsada, a ƙananan garuruwa kuma bai kai haka ba) da kuma yanayin muhallin da jami’ar take.
- Abinci: Sayen kayan abinci a shaguna ya fi sauƙi a kan cin abinci a restaurant.
- Zirga-Zirga: Tsarin zirga-zirga na gama-gari ya fi sauƙi da tattali a manyan birane irin Tehran.
- Data da Kati: Datar waya na da sauƙi a Iran, to amma sauri da inganci kan iya bambanta.
Wannan jadawalin ƙiyasi ne kawai, farashin rayuwa na iya bambanta tsakanin mutane, kowa da irin yanayin rayuwarsa.
Samun Admission a jami’o’in Iran cikin sauƙi
Da yawan jami’o’in ƙasar Iran na da sauƙin samun admission ga ɗaliban ƙasashen waje. Ta hanyar bayar da takardun karatu da wasu ƴan gajerun jarabawoyi, ɗalibai za su iya samun karɓuwa su kuma fara karatunsu nan take. Wannan na da matuƙar muhimmanci ga ɗaliban da basu da isashshen lokaci.
Damarmakin Ayyukan Bincike a Iran
Iran na ba ɗaliban ƙasashen waje damar gudanar da bincike mai inganci. Da yawan jami’o’i na da haɗin gwiwa da cibiyoyin bincike, inda sukan ba wa ɗalibai damar shiga ayyukan kimiyya. Wannan gogewa ba kawai tana faɗaɗa iliminsu ba ne, har ma tana iya zama hanya ta samun damar aiki a nan gaba.
Koyon Farsi
Karatu a Iran kan bada damar musamman ta koyon yaren Farisanci. Kasancewarsa yare mai ɗimbin tarihi da zurfin adabi, yaren farsi na daga cikin yaruka masu daɗi na duniya. Iya wannan yaren zai taimaka wa ɗalibai wurin zurfafa sanin al’adu da tarihin ƙasar Iran, kuma zai iya taimaka musu wurin samun damar aiki a gaba.
Karamcin Mutane
An shaidi Iraniyawa da son baƙi da fara’a. Ɗaliban ƙasashen waje kan samu kyakkyawar tarba daga mutanen gari (idan sun gan su). Wannan zai iya taimaka musu wurin sakin jiki da saurin sabawa da sabon muhallinsu.
Tarihi da Al’adu
Iran na cikin ƙasashe masu daɗaɗɗen tarihi a duniya. Akwai wuraren tarihi masu yawa a ƙasar. Ɗalibai na iya amfani da damarsu wurin ziyartar wuraren tarihi daban-daban irin su Persepolis, Pasargad, kasuwannin gargajiya, da sauransu domin sanin tarihin ƙasar.
Ayyukan Al’adu
A Iran, akan shirya taruka da bukukuwa na al’adu daban-daban wanda ɗalibai za su iya halarta. Shirin fil, bukukuwan shekara, baje kolin litattafai, da sauransu waɗanda halartar su zai iya taimakon ɗalibai wurin zamantakewa.
Ƙulla Alaƙoƙi na ƙasa da ƙasa
Karatu a Iran na iya taimakawa wurin gina alaƙoƙi tsakanin ƙasashe. Ɗalibai na zuwa Iran daga ƙasashe mabambanta, hakan na iya samar da damar aiki tare a tsakaninsu. Waɗannan alaƙoƙin na iya zama silar bunƙasa al’adunsu da sana’o’insu zuwa wasu ƙasashe.
Alaƙar Karatu
Jami’o’i da yawa na mu’amala da makarantun sauran ƙasashe kuma suna musharaka a projects ɗin ƙasa da ƙasa. Wannan mu’amalar na ba ma ɗalibai damar samun tajarubobin da za su amfane su nan gaba.
Rayuwar Zamantakewa
Yanayin rayuwar zamantakewa a Iran yana da ban sha’awa. Ɗalibai za su iya shiga ayyukan wasanni, ƙungiyoyin ɗalibai, da sauransu inda za su samu sabbin abokanai. Ire-Iren waɗannan ayyukan na taimaka musu wurin jin ɗaɗin rayuwarsu a makaranta.
Rufewa
A taƙaice, karatu a Iran bai taƙaitu a iya tajarubar makaranta yake ba ɗalibai ba, hadda gogewar al’adu. Ta hanyar binciko damarmakin da ke akwai a ƙasar Iran, ɗaliban ƙasashen waje na iya samun ƙarin sabbin tajarubobi wanɗansa za su amfane su a rayuwa.