Fita waje karatu ɗaya ne daga cikin abubuwan da ke yin tasiri a goben mutum. Saboda muhimmancin hakan ne ya sa yana da kyau kafin mutum ya yi bincike sosai game da ƙasar da yake son zuwa karatu. Zamaninnan ƙasashe na fuskantar kai-komo na mutane masu yawa tsakaninsu saboda mabambantan dalilai da suka haɗa da karatu, aiki, samun walwala, ko kuma gudun hijira saboda yaƙi ko matsalolin siyasa, da dai sauransu. Wasu ƙasashen da ke karɓar ƴan gudun hijira suna amfani da su a matsayin albarkatun ɗan’adam (human resources). A wannan rubutu za mu yi magana ne akan ƙasar Iran a wannan babin.
Gabatarwa:
Saboda matsayin ƙasar Iran a ilmance da manyan jami’o’i da take da su, mutane da yawa na da sha’awar su zo su yi karatu a Iran. A kowace shekara akwai adadi mai yawa na mutane da ke zuwa ƙasar Iran domin su yi karatu kuma bincike ya nuna cewa adadin yana daɗa hauhawa ne.
Kamanceceniyar yanayin iska da al’adu:
Iran na da busasshen yanayi a arewacin yankin equator. Nisan ƙasar daga manyan tekuna da yankunan kaɗawar iska shi ne ya sabbaba mata busasshen yanayi. Garin Tehran shi ne babban birnin tarayya na ƙasar, sunan kuɗinsu Riyal, addinin musulunci ne ke iko da ƙasar, sannan yaren farsi shi ne yaren ƙasar a hukumance. Ƙasar Iran (Jamhuriyar Musulunci ta Iran) ita ce ƙasa ta biyu a yankin gabas ta tsakiya sannan tana da larduka 31 a nahiyar Asia. Ƙasar Iran na kewaye da ƙasashen Iraq, Turkey, Armenistan, Azerbaijan, Turkmenistan, Afghanistan, da Pakistan. Hakazalika tana da iyaka a ruwa da ƙasashen Kazakhstan, UAE, Oman, Qatar, Saudi Arabia, Kuwait, da Russia.
Zaɓen ƙasa don neman aiki:
Daya daga cikin dalilan da ke sanya mutane barin ƙasashensu shi ne neman aiki, suna zuwa ne don neman aikin da zai ƙara inganta rayuwarsu da sama musu walwala. Ƙasashen da ke da raunin tattalin arziki ko ƙarancin damarmakin ɗaukar aiki ba su dace da irin waɗanna nau’in mutanen masu barin ƙasashensu ba. Amma saboda yanayin tsaro da aminci da ke ƙasar Iran da maƙotanta da kwanciyar hankali, ya sanya da yawa na kwaɗayin zuwa ƙasar aiki.
Yanayin kayan aiki da farashin kiwon lafiya da magani:
Maganar kayan aiki da farashin kiwon lafiyar jiki da ta tunani, magana ce mai muhimmanci wadda mutane na jinjina ta kafin su yanke shawara ta ƙarshe a kan ƙasar da za su tafi. Tun bayan yaƙin duniya na biyu an samu cigaba sosai a ɓangaren kiwon lafiya da ayyukan likitanci fiye da da, ta yadda an samu ragowar mace-mace sakamakon yaɗuwar cutuka bisa ga da. Tawagar likitanci ta ƙasar Iran ta samu nasarar rage dogaro da wasu ƙasashe a harkokin likitanci ta hanyar aiki tuƙuru da horar da ƙwararru a wannan fanni.
Yawon buɗe ido:
Ƙasar Iran na daga cikin ƙasashen da suka samu ci gaba a harkokin yawon buɗe ido a ƴan shekarunnan. Yawon buɗe ido na taka muhimmiyar rawa wurin bunƙasa tattalin arzikinta da kuma samar da aikin yi tare da wanzar da al’adunta. Iran ce ta goma a jerin ƙasashen duniya masu abubuwan jan hankali na yawon buɗe ido.
Daga cikin wuraren yawon buɗe ido na ƙasar Iran akwai: Ƙauyen Kandovan, Kariz Kish, tafkin Maharlo, Dasht Lot, masallacin Nasir Almalik, Darre Setaregan Qashm, shuɗin gine-ginen Jahan Shoshtar, tafkin Ganj, da sauransu… A kowace shekara waɗannan abubuwan na jan hankalin mutane masu yawon buɗe ido da dama zuwa ƙasar Iran.
Yanayin tsadar rayuwa shi ne babban abun dubawa kafin zuwa wata ƙasa:
Akwai babbar alaƙa tsakanin kasafin kuɗinku da kuma yanayin tsadar rayuwa a ƙasar da kuke son zuwa. A wasu ƙasashen akwai tsadar rayuwa sosai, farashin kuɗin masauki, kayan anbinci, zirga-zirga ya bambanta tsakanin ƙasashe. A ƙasar Iran, saboda yawan dogaronsu da abubuwan da suke samarwa a cikin gida da ƙoƙarinsu na ganin cewa sun rage amfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, ya samar da ragowa mai gwaɓi a farashin rayuwa a ƙasar.
Alaƙa da maƙota:
Ƙasar Iran na maƙotaka da jimillar ƙasahe 15 ta ƙasa da ta ruwa. Ƙasashen da ke maƙotaka da Iran ta ƙasa sun haɗa da:
_ Pakistan
_ Afghanistan
_ Turkmenistan
_ Republic of Azerbaijan
_ Armenistan
_ Turkey
_ Iraq
Ƙasashen da ke maƙotaka da Iran ta ruwa sun haɗa da:
_ Azerbaijan
_ Turkmenistan
_ Russia
_ Kazakhstan
_ UAE
_ Bahrain
_ Saudi Arabia
_ Oman
_ Qatar
_ Kuwait
_ Iraq
_ Pakistan
Fifikon ƙasar Iran
Bisa ranking na ƙarshe da aka yi a shekarar 2021, ƙasar Iran ta zo a matsayi na 15 a jerin ƙasashen ilimi na duniya.
Shigar jami’o’in Iran a fitattun tsarukan ranking na duniya:
Kodayake ranking ɗin jami’a ba shi ne ma’aunin haƙiƙa na gane matsayinta na ilimi ba. Wannan ne ya sanya aka samar da wasu tsarukan ranking na musamman irinsu:
Tsarin ranking na Shanghai: Shugaban ƙasar China na lokacin ya damu sosai a kan ayyukan jami’o’in ƙasa da ƙasa, wannan ne ya sanya aka samar da tsarin Shanghai a shekarar 1998. Daga lokacin aka riƙa sabunta natijojin binciken wannan tsarin a kowace shekara. Ma’aunan da ake amfani da su a wanna tsarin sun haɗa da; ingancin karatu, ingancin membobin tsangayar ilimi, natijojin ayyukan bincike, da kuma yanayin aikin jami’a a dunƙule. Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na TIMES: Ɗaya ne daga cikin tsarukan ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin ilimi na duniya wanda ya fara aiki a shekarar 2004. Shi kuma wannan tsarin na aiki da ma’aunai kamar haka; karatu (harabar karatu), bincike (yawan, kuɗin shiga, da shuhura), sanadodi (tasirin ayyukan bincike), kuɗin shiga daga masana’antu (ƙirƙira), da kuma kimar jami’a a idon duniya (ma’aikatanta, ɗalibanta, da ayyukanta na research). Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na QS: Shi ma wani tsarin ranking ne wanda ya fara aiki a matsayin haɗin gwiwa da tsarin TIMES daga shekarar 2004 zuwa 2009. Daga bisani ya ci gaba aiki a ƙashin kansa. Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na ISC: Ya fara aiki ne a shekarar 2010. Wannan tsarin ya bada ƙarfi wurin ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke ƙasashen musulunci ne. Shi kuma wannan tsarin ma’aunansa sun haɗa da; bincike (ingancin bincike, tasirin bincike, rijistar haruffa, yawa, yawan mujallun da aka wallafa, yawan littafan da membobin tsangayar ilimi suka wallafa, yawan tsare-tsare da yarjejeniyoyin bincike), karatu (membobin tsangayar ilimi da aka karrama, maƙaloli masu citations da yawa, alaƙar membobin tsangayar ilimi masu PhD da sauran membobi, graduates da suka samu karramawa, alaƙar membobin tsangayar ilimi masu matsayi da sauran membobi, alaƙar membobin tsangayar ilimi da ɗalibai, alaƙar tsakanin ɗaliban postgraduate da sauran ɗalibai, ɗalibai masu lambar yabo a wasannin olympics na duniya), kima a idon duniya (alaƙar tsakanin ɗaliban waje da sauran ɗaliban makarantar, alaƙar membobin tsangayar ilimi da suka yi karatun PhD a ƙasar waje da sauran membobi masu PhD, yawan tarukan ƙasa da ƙasa, musharaka a ayyukan ƙasa da ƙasa, yawan musharakar jami’a a wallafa maƙalolin ƙasa da ƙasa), kayan aiki _ walwala (jimillar yawan taken littafai idan an kwatanta da yawan ɗalibai, yawan cibiyoyi da ƙungiyoyin da sansanonin bincike), ayyuka wa al’umma, tattalin arziki da masana’antu (yawan ƙungiyoyi da kamfanoni, yawan cibiyoyin bunƙasawa, yawan cibiyoyi masu dogaro da ilimi). Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Jerin jami’o’in da ke ƙarƙashin ma’aikatar ilimi:
University of Tehran: Watakila ku yi tunanin abubuwan da ya kamata ku sani domin karatu a wannan jami’a. Tambayoyi kamar: Yawan kuɗin makaranta, kwasa-kwasan karatu, matakan karatu, kuɗin hostel ko masauki a Tehran, da sauransu. Domin samun bayanan da kuke buƙata a kan wannan jami’a, ku ziyarci rubutunmu mai take Karatu a University of Tehran.
_ Sharif University of Technology: Mutane na buƙatar masaniya da bayanai wajen zaɓar makaranta da fannin karatu, hakan zai basu damar yin zaɓi mai inganci a rayuwarsu. Taken wannan rubutun shi ne Karatu a Sharif University of Technology, wanda a ciki mun yi ƙoƙarin gabatar da jami’ar da matakinta na ilimi da sauran bayanan da suka shafe ta. Domin samun cikakken bayani, ku garzaya ku karanta rubutunmu mai suna Karatu a Sharif University of Technology.
_ Tarbiat Modares University: Karatu a jami’ar Tarbiat Modares wadda ita kaɗai ce jami’ar karatun postgraduates a Iran. Ku ziyarci wannan rubutu domin samun bayanai game da karatu a wannan jami’a; Karatu a Tarbiat Modares University.
_ Amirkabir University of Technology: Jami’ar Amirkabir ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in ƙasar Iran kuma ita ce jami’ar fasaha ta farko a Iran. Manufarmu a wannan rubutun ita ce bayyana muhimman abubuwa da suka shafi yanayin karatu a jami’ar Amirkabir domin suƙaƙe muku zaɓen makaranta. Ku ziyarci wannan maƙala domin samun cikakken bayani a kan jami’ar Amirkabir. Karatu a Amirkabir University.
_ Shiraz University: Daga cikin dalilan da ya sa mutane ke zuwa ƙasar Iran shi ne karatu. Jami’ar Shiraz jami’ar gwamnati ce kuma jami’a ce mai tarihi kuma ta farko-farko a matakin ƙasa da ƙasa, a garin Shiraz. Jami’ar na karɓar adadi mai yawa na ɗaliban ƙasar waje daga ƙasashe daban-daban na duniya ciki har da ɗaliban ƙasar Iraq. Saboda haka karanta wannan rubutun na da muhimmanci ga ɗaliban da ke sha’awar yin karatu a jami’ar Shiraz. Ku karanta wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da karatu a jami’ar Shiraz. Karatu a Shiraz University.
_ Iran University of Technology: A wannan rubutun kuma mun yi bayani ne a kan jami’ar kimiyya da fasaha ta Iran, bayanai game da yanayin karatu a makarantar da sharuɗan samun admission. Ku ziyarci wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da jami’ar. Karatu a Iran University of Science and Technology.
_ University of Tabriz: Garin Tabriz (gari na uku mafi girma a ƙasar Iran) na nan a yankin arewa maso yammacin ƙasar kuma shi ne cibiyar lardin Azarbaijan ta gabas. A garin ne jami’ar Tabriz take wadda ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in ƙasar Iran. Ku garzaya ku karanta rubutunmu mai suna Karatu a University of Tabriz domin samun cikakken bayani.
_ Ferdowsi University of Mashhad: Da yawan ɗalibai na fuskantar ƙalubale wajen zaɓen makarantar da za su yi karatu. Zaɓen jami’a ya kasance al’amari mafi muhimmanci ga ɗalibai. Sanin kowa ne makaranta kan iya canza rayuwar mutum. A wannan rubutu, za mu kawo muku bayani a kan janibobi daban-daban na karatu a Ferdowsi University kamar makarantunta, kwasa-kwasanta, kayan aikinta, da sauransu domin sauƙaƙe muku yin zaɓi mai kyau don ci gaba da karatunku. Ku karanta rubutunmu mai take Karatu a Ferdowsi University of Mashhad domin samun cikakken bayani.
_ Babol Noshirvani University of Technology: Idan kuna da sha’awar yin karatu a ƙasar Iran amma kuma suna shakka saboda tsadar kuɗin makaratnta, wannan jami’a zaɓi ne da ya kamata su yi la’akari da shi. Jami’ar ta Babol Noshirvani wadda aka mayar jami’ar fasaha ɗaya ce daga cikin jami’o’in fasaha na Iran masu daraja ta ɗaya a ƙasar. Har ila yau jami’ar na daga cikin jami’o’i da ke kiyaye sharuɗan karatu ɗari bisa ɗari. Za mu kawo muku ƙarin bayani game da jami’ar a cigaban rubutunmu. Domin samun cikakken bayani game da karatu a wannan jami’ar ku ziyarci rubutunmu mai take Karatu a Babol Noshirvani University of Technology.
_ University of Kashan: Jami’ar Kashan ita ce jami’a ta farko kuma jami’a mafi girma a Kashan na lardin Isfahan. Domin samun ƙarin bayani game da karatu a wannan jami’a kuna iya ziyartar rubutunmu mai taken Karatu a Jami’ar Kashan.
_ Shahid Beheshti University: Wata daga cikin sanannun jami’o’in ƙasar Iran kuma mai babban matsayi a ilmance ita ce jami’ar Shahid Beheshti. Za ku samu cikakken bayani game da yanayin karatu da sharuɗan karɓar ɗalibai a jami’ar a rubutunmu na Karatu a Shahid Beheshti University.
_ Yasouj University: Garin Yasouj shi ne cibiyar lardin Kuhgeluyeh Boyer-Ahmad. Garin Yasouj yana kan tudun Zagros a ƙololuwar Dana, tsayin mita 1870 daga teku. Ana kiran mutanen wannan garin da suna ‘Ler’. Akwan cibiyoyin karatu da jami’o’i 16 a wannan gari, jami’ar gwamnati ta Yasouj na ɗaya daga cikin su. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Yasouj University domin samun cikakken bayani.
_ University of Maragheh: Wannan jami’a ce ta gwamnati a garin Maragheh da ke lardin Azarbijan ta Gabas. Ku ziyarci rubutunmu na Karatu a University of Maragheh domin samun cikakken bayani.
_ Azarbaijan Shahid Madani University: Ɗaya ce daga cikin jami’o’in ma’aikatar ilimi a lardin Azarbaijan Sharqi. Manufarmu a wannan rubutu ita ce gabatar da bayani gameda jami’ar Shahid Madani, tarihinta, ranking, kwasa-kwasan da ake yi a cikinta, makarantunta, kuɗaɗen makaranta, da sauransu… Yanke hukunci akan inda zamu yi karatu abu ne mai matuƙar muhimmanci saboda hakan zai taka muhimmiyar rawa wurin gina gobenmu. Za ku samu cikakken bayani a rubutunmu na Karatu a Jami’ar Shahid Madani.
_ University of Kurdistan: Lardin Kurdistan da ke yammacin ƙasar Iran yana da iyaka ta kimanin kilomita 200 da ƙasar Iraq. Babban birnin wannan lardin shi ne Sanandaj. Ku karanta rubutunmu na Karatu a University of Kurdistan domin samun ƙarin bayani.
_ University of Mohaghegh Ardabili: Garin Ardabil na a yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran kuma jami’ar Mohaghegh Ardabili ita ce kaɗai cikakkiyar jami’a a garin. Ku karanta rubutun Karatu a University of Mohaghegh Ardabili domin samun cikakken bayani game da ita.
_ Islamic Azad University Najafabad: Isfahan (gari na uku mafi yawan jama’a a Iran) babban gari ne na tarihi a tsakiyar ƙasar Iran. A wannan gari jami’ar Azad Najafabad take. Idan kana cikin mutanen da ke tunanin yin karatu a wannan jami’a, za ka iya karanta rubutunmu na Karatu a Islamic Azad University Najafabad domin samun ƙarin bayanai a kanta.
_ Isfahan University of Technology: Zaɓen makaranta da kwas ɗin karatu abu ne mai matuƙar muhimmanci ga ɗalibai. A wannan rubutu za mu yi magana game da yanayin karatu a jami’ar fasaha ta Isfahan da abubuwa daban-daban da suka shafi hakan. Mun kawo bayani a kan makarantu, kuɗin makaranta, kuɗin hostel, maƙaloli da ranking ɗin jami’ar duk domin ku samu sauƙi wurin tantancewa. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Isfahan University of Technology domin samun cikakken bayani.
_ Sahand University of Technology: Ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in fasaha na ƙasar Iran. Mun kawo muhimman bayanai da suka shafi karatu a wannan jami’a, bayanai kamar tarihinta, kwasa-kwasanta, abubuwan more rayuwa, nasarori, da sauransu duk domin sauƙaƙe muku bincike a kanta. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Sahand University of Technology domin samun bayanan.
_ Shiraz University of Technology: Jami’ar gwamnati ce a garin Shiraz da ke lardin Fars (lardi na 4 mafi yawan jama’a). Ku karanta wannan rubutun domin samun bayanai game da yanayin karatu a wannan jami’a. Karatu a Shiraz University of Technology.
Jarin jami’o’in da ke ƙarƙashin Hukumar Lafiya:
_ Tehran University of Medical Science: Karatu a wannan jami’a (wadda ke garin Tehran) a matsayin ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati, wadda matsayinta a ilmance idan an kwatanta da sauran jami’o’i yana kwaɗaitar da mutane masu yawa zuwa bincike a kanta. Jami’ar na ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, jinya da karatun likitanci. Ku karanta wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da jami’ar Karatu a Tehran University of Medical Science.
_ Shahid Beheshti University of Medical Science: Bayani a kan wannan jami’a na da muhimmanci saboda yadda ɗalibai ke kwaɗayin karatu a cikinta saboda tasirin da zai yi a wurin gina rayuwarsu, bayani a kan tarihinta, kwasa-kwasanta, makarantunta da sauransu. Ku karanta rubutun Karatu a Shahid Beheshti University of Medical Science domin samun waɗannan bayanai.
_ Iran University of Medical Science: Ɗaya ce daga cikin jami’o’in likitanci na ƙasar Iran masu babban matsayi a ilmance. Domin samun bayani game da sharuɗan karɓar ɗalibai a wannan jami’a a matsayinta na ɗaya daga cikin zaƙwaƙuran jami’o’in ƙasar Iran, bayanai da suka shafi yanayin karatu a cikinta da sauran bayanai, ku karanta maƙalarmu ta Karatu a Iran University of Medical Science.
_ Mazandaran University of Medical Science: Mazandaran lardi ne a arewacin ƙasar Iran wanda a cikinsa akwai wata jami’ar likitanci da ke garin Sari. Ku garzaya wannan maƙala ta Karatu a Mazandaran University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Kurdistan University of Medical Science: Ita wannan jami’a cibiya ce ta koyarwa da ayyukan kiwon lafiya a garin Sanandaj lardin Kurdistan. Ku karanta rubutun Karatu a Kurdistan University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Urmia University of Medical Sciences: Garin Urmia ne cibiyar lardin Azarbaijan Gharbi, a yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran. Wannan jami’a ɗaya ce daga cikin jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke cikin garin. Ku karanta rubutun Karatu a Urmia University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Ahvaz Jundishapur University of Medical Sciences:
_ Kashan University of Medical Sciences: Tana ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya a garin Kashan. An gina makarantar likitanci ta Kashan University of Medical Sciences and Healthcare Services a fili mai girman murabba’in mita 22610. Bayanai game da jami’ar likitanci ta Kashan na da muhimmanci ga mutane. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Kashan University of Medical Sciences domin samun waɗannan bayanan.
_ Mashhad University of Medical Sciences: Garin Mashhad ne cibiyar lalrdin Khorasan Razavi a arewa maso gabacin ƙasar Iran. Saboda haramin Imam Rida (a) da ke wannan gari, garin Mashhad ya kasance abun girmamawa ga musulmi tun zamanin bayan kuma a kowace shekara garin na karɓar baƙuncin ɗimbin baƙi da maziyarta. Hakazalika garin na da babban matsayi a ilmance da al’adance. Akwai ingantattun jami’o’i masu yawa a wannan gari, Mashhad University of Medical Science ɗaya ce daga cikinsu. Ku karanta rubutun Karatu a University of Medical Sciences domin samun ƙarin bayani.
_ Tabriz University of Medical Sciences: Garin Tabriz na nan a lardin Azarbaijan Sharqi a yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran. Ana kallon garin a matsayin gari na 3 mafi girma a ƙasar Iran. Daga cikin jami’o’in da ke cikin garin Tabriz akwai Tabriz University of Medical Sciences wadda tana ƙarƙashin hukumar lafiya, jinya da karatun likitanci ta Iran. Duba da tarihinta, matsayinta a ilmance, malamanta, kayan aikinta, jami’ar na iya zamowa damar cigaba da gogewa ga mutane da kuma silar kai wa ga hadafofinsu. Kuna iya samun bayanai game da jami’ar a rubutunmu na Karatu a Tabriz University of Medical Sciences.
_ Isfahan University of Medical Sciences: Lardin Isfahan na da mabambantan jami’o’i da cibiyoyin ilimi kamar dai sauran lardukan. Jami’ar Isfahan University of Medical Sciences ɗaya ce daga cikin cibiyoyin ilimi 67 da ke akwai a lardin. Ku bibiyi wannan rubutun Karatu a Isfahan University of Medical Sciences domin samun ƙarin bayani.
_ Kerman University of Medical Sciences: Garin Kerman babban gari ne a Iran. Sanadiyyar samuwar wannan jami’a a garin da irin ayyukan likitanci masu wuya da take yi na dashen gaɓoɓi da sassan jikin ɗan’adam, yanzu haka garin Kerman ya zama sansanin aikin likitanci na ƙasar Iran. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Kerman University of Medical Sciences domin samun cikakken bayani a kan wanna jami’ar.
_ Shiraz University of Medical Sciences: Bisa la’akari da kayan aiki, kwasa-kwasai, karɓar ɗalibai a dukan matakan karatu, samun gurbin karatu a wannan jami’a na da muhimmanci sosai ga ɗalibai. Kuna iya ziyartar wannan rubutu na Karatu a Shiraz University of Medical Sciences domin samun cikakken bayani game da wannan jami’ar.
Ƙasar Iran ta zo a matsayi na 20 tsakanin ƙasashen duniya a wajen karɓar ɗalibai wanda hakan babban cigaba ne ga ƙasar a fagen ɗaukar ɗaliban ƙasashen waje idan an kwatanta da shekarun baya. Samuwar ɗaliban wasu ƙasashe a wata ƙasa kan haifar da bunƙasar al’adun al’ummar ƙasar, da haɓakar matsayin cibiyoyinta na ilimi da ingancinsu, yana kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasar. Hakan ya sa ƙasashe da dama ke ta neman hanyoyin da za su ja hankalin ɗaliban wasu ƙasashe zuwa ƙasarsu. Yanzu haka akwai kimanin ɗaliban waje guda 95,000 da ke karatu a Iran. Kashi 75 a ciki ɗaliban postgraduate ne (kashi 50 ɗaliban PhD ne) kashi 30 kuma ɗaliban Master’s.
Alfanun Karatu a Iran:
_ Kuɗin makaranta na da sauƙi idan an kwatanta da sauran ƙasashe
_ Akwai damar karanta mabambantan kwasa-kwasai a mabambantan jami’o’i
_ Karatu a ƙasa mai mabambantan al’adu da yaruka
_ Akwai tsaro sosai fiye da sauran ƙasashen yankin
_ Abubuwan jan hankali na tarihi, ɗabi’a, da al’ada
_ Sauƙin samun kayan karatu da resources na ilimi
_ Sauƙin ayyukan kiwon lafiya da magani
_Da sauransu…
Cibiyoyin magani da asibitocin ƙasar Iran
_ Asibitin Bahman
_ Asibitin Pars
_ Asibitin Shahid Dr. Rahnamod
_ Asibitin Razavi ta Mashhad
_ Asibitin Sayyedal Shohada Yazd
_ Asibitin Shahid Sadoughi
_ Asibirin Erfan
_ Asibitin Askarieh
_ Asibitin Parsian
_ Asibitin Tehran
_ Asibitin Shahid Rajaei
_ Asibitin Noor da ƙwararrun cibiyoyin ido
_ Asibitin Milad
_ Asibitin Imam Sajjad (AS)
_ Asibitin Shahid Beheshti
_ Asibitin Shahid Dastgheib
_ Da sauransu…
Cibiyoyin kasuwanci na Iran:
_ Cibiyar kasuwanci ta Sam Center
_ Isfahan City Center
_ ARG Shopping Center
_ Khalij Fars Shopping Center Shiraz
_ Palladium Mall Tehran
_ Arg Shopping Center, Tajrish
_ Galleria Shopping Center
_ Tandis Shopping Center
_ Kourosh Shopping Mall
_ Rosha Shopping Mall
_ Sky Center Lavastan
_ Elahiyeh Shopping Center
_ Atlas Mall
_ Bamland
_ Aran Shopping Center
Hotel da masaukai a ƙasar Iran:
_ Esteghlal Hotel Tehran
_ Avin Hotel Tehran
_ Espinas Palace Hotel
_ Homa Hotel Tehran
_ Laleh Hotel
_ Wisteria Hotel Tehran
_ Ghasr Hotel Mashhad
_ Madinah Al-Reza Hotel
_ Homa Hotel Mashhad
_ Pars Hotel Mashhad
_ Chamran Grand Hotel
_ Zandiyeh Hotel Shiraz
_ Elysee Hotel Shiraz
_ Elgoli Pars Hotel Tabriz
_ Laleh Kandovan Hotel Tabriz
_ Abbasi Hotel Isfahan
_ Safaiyeh Hotel Yazd
_ Ramsar Parsian Hotel
_ Kerman Hotel
_ Da sauransu…