Garin Gorgan shi ne cibiyar lardin Golestan. Garin na a wani wuri mai tsayin mita 160 daga saman teku a arewacin ƙasar Iran. Lardin Golestan na da garuruwa 4, birane 2, da ƙauyuka 98. Manufarmu a wannan rubutu ita ce bayyana muku yanayin rayuwa, yanayin karatu, yanayin iska, yawon buɗe ido, da sauransu na garin Gorgan.
Gorgan
Masana tarihi sun tafi a kan cewa bayan ƙabilun Aryan sun yi hijira zuwa Iran, wasunsu sun zauna a garin Hyrkana (Gorgan), sannan shaidun tarihi sun nuna cewa an zauna wurin shekaru dubu shida da suka wuce. Sunan Gorgan na da “Estrabad”, ana kiranta da wannan sunan har zuwa shekarar 1937.
Gorgan na cikin koren garuruwan arewacin ƙasar Iran. Daga arewa garin Gorgan na iyaka da garuruwan Aqqla da Turkman, ta kudu garin Semnan, ta yamma Mazandaran, ta gabas kuma lardin Khorasan Razavi.
Kashi 30% na mutanen wannan gari sun zo ne daga ƙauyuka. A aikin ƙidaya da aka gudanar a shekarar 2016, an ƙirga mutum 350676 mazauna garin Gorgan.
Ta fuskar yanayin ɗabi’a kuma, garin Gorgan na da yankuna biyu; tsaunuka da sarari. Garin Gorgan na da matsakaicin yanayi (matsakaicin awon ruwan sama da ke sauka a kowace shekara shi ne milimita 5838). Akwai ƙarancin gurɓacewar iska a garin saɓanin sauran garuruwan arewacin Iran.
Kamar dai sauran garuruwa, Gorgan na da nau’o’in tsaraba daban-daban. Tsarabar da aka fi so daga garin Gorgan ita ce kayan zaƙinsu na gargajiya irin su burodin citta, burodin dabino, Halwa, Sarghabili, burodin Shirmal, da sauransu. Wasu daga cikin tsarabobin garin Gorgan sun haɗa da; dardumar Turkman da yadin saƙa.
Har ila yau, garin Gorgan na ɗauke da mabambantan ƙabilu irin su Sadate Estar Abadi, Mazni, Baluch, Sistan, Turk (mutanen Azarbaijan, Qazlbash, Turkman, Qazaq) da baƙin da suka zo daga wasu larduka kamar Semnan da Khorasan.
Mutanen Gorgan na magana da harsuna 4 na Tabari Gorgani, Farsi, Ziyarati, da Katoli.
Karatu a Gorgan
Akwai jimillar cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 30 a lardin Golestan ɗauke da ɗalibai 60854 da malamai 2562. Bincike ya nuna cewa an wallafa maƙalolin ilimi 36441 ciki har da maƙalolin mujalla guda 7661 da na tarukan ilimi guda 21049, da wasu maƙalolin a matakin ƙasa da ƙasa. Daga cikin ingantattun cibiyoyin ilimi na lardin Golestan akwai Jami’ar Golestan wadda ke cikin garin Gorgan. Za ku iya samun ƙarin bayani a rubutunmu mai suna Karatu a Golestan University.
Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido
Akwai wuraren yawon buɗe ido masu yawa a ƙasar Iran wanda kowanensu ya keɓantu da wasu abubuwan burgewa. Gorgan na ciki garuruwa masu kyau a arewacin Iran, cike yake da abubuwan nishaɗi da yawon buɗe ido kuma a kowace shekara ana maziyarta masu zuwa da yawa. Abubuwan kallo na ɗabi’a na wannan gari sun fi yawa a kan na sauran garuruwan arewacin Iran. A cigaba za mu kawo muku sunayen wuraren yawon buɗe ido na wannan gari.
- Fadar Tarihi
- Fadar Agha Muhammadkhan Qajar
- Gidan Bagheri
- Gidan Shirangi
- Madrase Emadieh
- Gidan Amir Latifi (gidan tarihi na masana’antun hannu)
- Karvansarae Qazlaq
- Babban Masallaci
- Tudun Narges
- Imamzadeh Roshan Abad
- Imamzadeh Noor
- Masallacin Golshan
- Gidan Ramezan Ali Khorasan
- Barankouh Waterfall
- Naharkhoran Park
- Dajin Alangdarreh
- Ƙauyen Ziyarat
- Rango waterfall
- Abandan Tushan
- Khalij
- Madatsar ruwa ta Nowmal
- Da sauransu
Cibiyoyin magani da asibitoci
_ Asibitin Mas’ud
_ Asibitin Mateghe’i
_ Asibitin Ayatollah Taleghani
_ Clinic ɗin musamman na Dezyani
_ Asibitin Dr. Musawi
_ Asibitin Panjom Azad
_ Asibitin Falsafi
_ Asibitin Hakim Jorjani
_ Asibitin musamman na Parsiyan
_ Asibitin Sayyad Shirazi
_ Asibitin zuciya na Shifa
_ Asibitin yara na Taleghani
_ Asibitin ƙuna
_ Da sauransu…
Hotel Hotel na garin Gorgan
_ Botanic Hotel
_ Azin Hotel
_ Jahangardi Hotel
_ Ziyarat Hotel
_ Khayyam Hotel
_ Gol Narges Hotel
_ Atlas Hotel
_ Pardis Hotel
_ Farhangian Hotel
_ Shanli Hotel
_ Da sauransu…
Laburaruka
_ Laburaren gari na Bosharat
_ Laburaren Gari na Hafez
_ Laburaren gari na Mirdamad
_ Laburaren gari na Mirfenreski
Cibiyoyin Kasuwanci
_ Warkana Shopping Center
_ Royal Shopping Center
_ Zartasht Shopping Complex
_ Capri Shopping Center
_ Tandis Shopping Center
_ Morsel Shopping Complex
_ Silvana Shopping Center
_Da sauransu…
Gidajen cin abinci
_ Baranak Restaurant
_ Espinas Restaurant Cafe
_ Meykhosh Restaurant
_ Sun Palace Restaurant
_ Eros Restaurant
_ Behesht Hirkan Restaurant
_ Baba Taher Restaurant
_ Shukouh Darya Restaurant
_ Sufi Restaurant
_ Da sauransu…