Gorgan ɗaya ne daga cikin garuruwan jihar Goestan a ƙasar Iran wanda ke arewacin duwatsun Alborz, kuma kudancin tafkin Caspian. A wannan rubutu mai taken ‘Karatu a Golestan University’, zamu tsunduma cikin bayani game da ɗaya daga cikin makarantun gwamnati na ƙasar Iran wato Golestan University.
Gabatarwa
Golestan University ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati wadda aka assasa a shekarar 2008, a lardin Golestan.
Akwai ɗalibai 3700, malamai 230, da mambobin kwamitin ilimi 170 a wannan cibiyar. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi guda 3104 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida,[1036 مقاله ژورنالی و 2068 مقاله کنفرانسی] da kuma maƙala 1286 a matakin ƙasa da ƙasa. Hakazalika jami’ar ce mawallafiyar mujalla 3 na musamman. Zuwa yanzu an gudanarda manyan taruka 7 a cikin wannan jami’ar.
A ranking na jami’o’in ƙasar Iran da aka yi a shekarar 2022, Jami’ar Golestan ta samu matsayi na 51.
Makarantu
_School of Sciences
_Faculty of Humanities and Social Sciences
_Gorgan Technical and Engineering College
_Aliabad Technical and Engineering College
Gorgan School of Technical and Engineering dake titin Al-Ghadir
Kwasa-Kwasai
_Biology
_Biochemistry
_Geology
_Mathematics and Applications
_Mathematical Statistics
_Physics
_Geography
_Business Management
_Economy
_Law
_Electric Engineering
_Civil Engineering
_Computer Engineering
_Architectural Engineering
_Chemical Engineering
_Mechanical Engineering
_Natural Hazards
_Shia Studies
_Geography and Urban Planning
_Psychology
_The History of the Islamic Revolution
_Sport Sciences
_Meteorology
_Persian Language and Literature
_English Language and Literature
_Physical Chemistry
_Tectonics
_Applied Chemistry
_Da sauransu…
Domin samun list ɗin kwasa-kwasan da akeyi a wannan jami’ar da matakan karatu, ku sauke wannan fayil ɗin:
Kwasa-Kwasan Golestan University
Kuɗin Makarantar Golestan University
Ababen More Rayuwa
Hostel: Golestan University batada hostel, amma tana da wuraren kwana masu zaman kansu a Aliabad da Gorgan. A cikin garin Gorgan, akwai gidan baƙi 3 na maza, 4 na mata, a garin Aliabad kuma akwai guda 2 na mata. Gidajen baƙi nada abubuwa kamar gadaje, firiji, na’urorin sanyayawa da ɗumama wuri, da sauran abubuwa.
Babban Laburare: An buɗa babban laburaren wannan jami’a ne a watan Janairun shekarar 2010, a daidai lokacin tunawa da juyin musulunci na Iran. Zuwa yanzu wannan laburaren yana gudanar da ayyukansa ne a harabar jami’ar dake titin Shahid Beheshti.
Nasarorin Jami’a
_Zakarun gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a fagen mita 100×4, da kuma samun wani kaso a gasar olympics ta wasanni karo na 14 a faɗin ƙasar.
_Samun Matsayi na 2 a gasar chess wadda Gorgan University of Agricultural Sciences and Natural Resources ta shirya
_Samun matsayi na 4 a gasar Volleyball wadda University of Guilan ta shirya
_Samun matsayi na 3 da ɗalibin wannan jami’ar yayi a gasar kokawa ta ƙasa da ƙasa wadda ƙasar Rasha ta shirya.
_Da sauransu…
Adireshi
Adireshi: Golestan University _ Titin Shahid Beheshti _ Gorgan _ Golestan
Tambayoyin da ake yawan yi
- Shin za’a iya karɓar Bizar karatu a wannan Jami’a?
Eh - Ko akwai wurin kwana na masu iyali a wannan jami’ar?
A’a, saidai wurin kwanan ɗaliban da basuda aure.
[neshan-map id=”25″]