[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Madogarar bayanai a kan scholarship a Iran

Madogarar bayanai a kan scholarship a Iran

Loading

Minene scholarship? Wasu irin mutane ake ba scholarship? Ko kuna neman jagoranci game da al’amarin scholarship a Iran? Ku karanta wannan rubutun domin samun amsoshin waɗannan tambayoyin da kuma samun cikakken bayani game da tallafin karatu a ƙasar Iran.

Minene scholarship?

Amsa mafi sauƙi ga wannan tambaya ita ce: Idan kun samu admission a wata makaranta sai ya zamana an yi muku rangwame ko tallafi saboda ku samu sauƙin kashe kuɗi a makaranta, kuɗaɗe kamar; kuɗin sayen littafai, kuɗin hostel, da sauran kuɗin da suka shafi karatu, to an baku scholarship (wato tallafin karatu) kenan.

منح دراسية في ايران

Matakan samun scholarship

Bayan kun ga irin kalar scholarship ɗin da kuke buƙata, sai kuma tura buƙatar neman scholarship ɗin tare da takardunku. Ga yadda ake tura buƙatar neman scholarship:

  1. Za ku yi bincike har sai kun ga irin kalar scholarship ɗin da ya dace da ku.
  2. A wannan marhalar ne za ku shirya CV na karatunku domin gamsar da malaman makarantar da kuke nema. A cikin wannan cv ne za ku rubuta duka maƙalolin da kuka wallafa na ilimi, takardun shaidarku, baiwoyinku, da duk wani abu da kuka san zai ƙara muku tagomashi wurin samun wannan scholarship ɗin tare da kiyaye ƙa’idojin rubutu.
  3. Bayan cv, sai motivation letter da kuma duka takardun shaidar kammala karatunku tare da sakamako, su ma duk ku haɗa ku tura. Haka idan kuna da wata takarda da ke nuna ƙarancin ƙarfin tattalin arzikinku ko na iyalanku kuna iya turawa da ita.
  4. Bayan tura buƙatar, sai ku jira amsar samun karɓuwarta ko akasin haka tare da bibiyar halin da take ciki.
  5. Sai kuma shirin tantance takardunku domin tafiya ƙasar da za ku je.
  6. Idan an baku scholarship, dole sai kun jira an tura muku da admission letter ita ma.

Jami’o’in ƙasar Iran masu sauƙin kuɗin makaranta

Jami’aRanking ɗin Times
Azarbaijan Shahid Madani University601-800
Shahid Bahonar University of Kerman (Jami’ar Shahid Bahonar ta Kerman)1201-1500
Hakim Sabzevari University1001-1200
Kermanshah University of Medical Sciences501-600
University of Tabriz601-800
University of Maragheh1001-1200
Golestan University of Medical Sciences351-400

Takardun da ake buƙata domin neman scholarship

Takardun da ake buƙata a mafi yawan jami’o’in ƙasar Iran domin neman tallafin karatu (scholarship) sun dogara da irin kalar scholarship ɗin da aka nema.

  • Tura hoton fasfo (interanatinal passport)
  • Ƙaramin hoto
  • Sikanin na hoton transcript (na duka matakan karatun da aka gama) a harshen turanci
  • Recommendation letter da Motivational letter
  • CV

CV ɗinku ya kan ƙunshi bayanai a kan matakin karatunku tare da irin ayyukan da kuka ƙware akai, yana da tasiri sosan gaske a wurin neman scholarship

Ku tabbata cewa kun tanadi duka waɗannan takardun da aka buƙata don gudun samun matsala Idan akwai takardar da ba ku da, kuna iya tuntuɓarmu domin samun bayani a kan yadda za ku samu takardar.

منح دراسية في ايران

Jami’o’in da ma’aikatar Ilimi ta ƙasar Iraq ta amince da su

Kamar yadda kuka sani cewa ma’aikatar ilimi ta ƙasar Iraq ta bayyana wasu jami’o’in ƙasar Iran waɗanda ta tantance kuma ta ba ma ɗaliban ƙasarta damar su yi karatu a cikinsu. Jami’o’in da ke wannan list ɗin sun kasu gida biyu; “Jami’o’in Ebte’as” da “Jami’o’in Nafaqe Khaseh”. Mun kawo muku jadawali a ƙasa wanda zai yi muku jagoranci wurin zaɓen jami’ar da kuke so ku nemi scholarship a cikinta. (Wannan ya shafi ɗaliban ƙasar Iraƙi ne kawai)

Jadawalin Jami’o’in Ebte’as na shekarar 2023

التسلسلSunan Jami’o’in Ebte’as a harshen larabciSunan Jami’o’in Ebte’as a harshen turanci
1جامعة طهرانUniversity of Tehran
2جامعة طهران للعلوم الطبيةTehran University of Medical Sciences
3جامعة تربية مدرسTarbiat Modares University
4جامعة أمير كبير الصناعية(التكنولوجية)Amirkabir University of Technology
5جامعة شريف الصناعية(التكنولوجية)Sharif University of Technology
6جامعة شهيد بهشتي للعلوم الطبيةShahid Beheshti University of Medical Sciences
7جامعة علم وصناعة إيرانIran University of Science & Technology
8جامعة مشهد للعلوم الطبيةMashhad University Medical Science
9جامعة فردوسي مشهدFerdowsi University of Mashhad
10جامعة إيران للعلوم الطبيةIran University of Medical Sciences
11جامعة تبريزUniversity of Tabriz
12جامعة غلستان للعلوم الطبيةGolestan University of Medical Sciences
13جامعة كردستان للعلوم الطبيةKurdistan University of Medical Sciences
14جامعة مازندران للعلوم الطبيةMazandaran University of Medical Sciences
15جامعة أراك للعلوم الطبيةArak University of Medical Sciences
16جامعة بابل للعلوم الطبيةBabol University of Medical Sciences
17جامعة نوشيرواني بابل الصناعية(التكنولوجية)Babol Noshirvani University of Technology
18جامعة قزوين للعلوم الطبيةQazvin University of Medical Sciences
19جامعة قم للعلوم الطبيةQom University of Medical Sciences
20جامعة أرومية للعلوم الطبيةUrmia University of Medical Sciences
Sabuntawa ta ƙarshe; watan July, 2023

Jadawalin jami’o’in Nafaqeh Khaseh na shekarar 2023

التسلسلSunan Jami’o’in Nafaqeh Khaseh a harshen larabciSunan Jami’o’in Nafaqeh Khaseh a harshen turanci
1جامعة آزاد – نجف آبادIslamic Azad University, Najafabad Branch (IAUN)
2جامعة كاشان للعلوم الطبيةKashan University of Medical Sciences and Health Services
3جامعة كرمانشاه للعلوم الطبيةKermanshah University of Medical Sciences
4جامعة شيراز التكنولوجية(الصناعية)Shiraz University of Technology
5جامعة جندي شابور أهواز للعلوم الطبيةAhvaz Jundishapur University of Medical Sciences (AJUMS)
6جامعة شهيد مدني آذربايجانAzarbaijan Shahid Madani University
7جامعة إيلام للعلوم الطبيةIlam University of Medical Sciences
8جامعة كاشانUniversity of Kashan
9جامعة كردستانUniversity of Kurdistan
10جامعة المحقق الأردبيليUniversity of Mohaghegh Ardabili
11جامعة تبريز للعلوم الطبيةTabriz University of Medical Sciences
12جامعة كرمان للعلوم الطبيةKerman University of Medical Sciences
13جامعة شهيد بهشتيShahid Beheshti University
14جامعة شيرازShiraz University
15جامعة شيراز للعلوم الطبيةShiraz University of Medical Sciences
16جامعة الحكيم السبزواريHakim Sabzevari University
17جامعة إصفهان للعلوم الطبيةIsfahan University of Medical Sciences
18جامعة إصفهان التكنولوجية(الصناعية)Isfahan University of Technology
19جامعة خواجة نصير الدين طوسي التكنولوجية(الصناعية)K.N. Toosi University of Technology
20جامعة لرستانLorestan University
21جامعة مراغةUniversity of Maragheh
22جامعة مازندرانUniversity of Mazandaran
23جامعة سهند التكنولوجية(الصناعية)Sahand University of Technology
24جامعة سمنان للعلوم الطبيةSemnan University of Medical Sciences and Health Services
25جامعة شهركردShahrekord University
26جامعة شاهرود التكنولوجية(الصناعية)Shahrood University of Technology
27جامعة الرعاية الإجتماعية وعلوم التأهيلUniversity of Social Welfare and Rehabilitation Sciences
28جامعة أروميةUrmia University
29جامعة ياسوجYasouj University
30جامعة أراكArak University
31جامعة بو علي سيناBu-Ali Sina University
32جامعة دامغانDamghan University
33جامعة إصفهانUniversity of Isfahan
34جامعة خوارزميKharazmi University
35جامعة الخليج الفارسيPersian Gulf University
36جامعة سمنانSemnan University
37جامعة شاهدShahed University
38جامعة شهيد باهنر كرمانShahid Bahonar University of Kerman
39جامعة شهيد جمران أهواز​Shahid Chamran University of Ahvaz
40جامعة تربية معلم شهيد رجائيShahid Rajaee Teacher Training University
41جامعة البترول التكنولوجية(الصناعية)Petroleum University of Technology
Sabuntawa ta ƙarshe; watan July, 2023

Sharuɗan da ake buƙata wajen neman scholarship

Ɗaya daga cikin abubuwan da masu neman scholarship suka damu da su shi ne yadda za su ƙara yawan damarsu ta samun scholarship ɗin. Neman scholarship abu ne da yake fuskantar gasa a kowane lokaci. Daga cikin muhimman abubuwa masu tasiri a al’amarin scholarship akwai maki mai yawa, maƙaloli, makin yare, da sauransu.

  • Shekarun mai neman scholarship: Shekarun mutum na ɗaya daga cikin sharuɗan da dole sai an duba su. Iya ƙarancin shekarun mutum iya yawan damarsa ta samun scholarship a matakin digiri. A matakin masters shekara 24, PhD kuma wuraren shekara 30.
  • Karatu a ingantattun jami’o’i: A kowace ƙasa akwai jami’o’in da aka ware a matsayin fitattun jami’o’in masu daraja ta ɗaya bisa la’akari da ƙa’idoji da ma’aunan ƙasa da ƙasa waɗanda jami’o’in wasu ƙasashen ke kallo da ƙima fiye da sauran jami’o’in ƙasar. A wannan bagiren, karatu a manyan jami’o’i da makarantu yana taka muhimmiyar rawa a wurin samun scholarship.
  • Gabatar da maƙalolin ƙasa da ƙasa (ISI) da tsarukan bincike: Babu shakka gabatar da maƙalolin ƙasa da ƙasa waɗanda aka wallafa a ingantattun mujallu, yana taimaka wa ɗalibai sosai a wajen yaƙinsu na neman scholarship. Hakazalika gabatar da cv na ayyukan bincike da ke da alaƙa da fannin da mutum yake so ya karanta, shi ma yana tasiri sosai.
  • Maki da shaidar koyon yaren farsi ko turanci: Cimma sharaɗin maki dama abu ne da yake lazim a wajen neman scholarship. Mutanen da ke da GPA na first-class (85%) damarsu ta samun scholarship ta fi yawa. Haka kuma daga cikin takardu masu muhimmanci a wannan bagiren akwai takardar shaidar yaren farsi ko turanci.
  • Mu’amala da malamai: Daga cikin abubuwan da ke tasiri a damar samun scholarship akwai alaƙar ɗalibi da malaman makarantar da yake nema. Malamai na iya zaɓen ɗaliban da suka gamsu da su ta hanyar gurbin da ake basu a kowace shekara. Idan kuna son samun scholarship ta hanyar malamai dole ne ku rubuta proposal na research mai kyau kuma mai alaƙa da fanninku ku turawa malaman.

A wasu matakan karatu ne ake bayar da scholarship?

Damar samun scholarship ta fi yawa a matakin masters da PhD.

Ko sharaɗin shekaru na da muhimmanci a wurin neman scholarship?

Eh, a ƙasar Iran yana da muhimmanci.

Ko zai yiwu a nemi scholarship a makarantu daban-daban a lokaci ɗaya?

Eh, za ku iya neman scholarship a makarantu daban-daban a lokaci ɗaya domin jaraba sa’arku.

Related Posts
Leave a Reply